Zaɓe mai ɗumbin tarihi na gudana a Gambia

Kasar Gambia Hakkin mallakar hoto SEYLLOU/AFP/GETTY IMAGES
Image caption Jama'ar Gambian na fatan shia sabon babin siyasa a kasar

Al'ummar Gambia na kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen 'yan majalisar dokokin ƙasar ranar Alhamis, karon farko tun bayan sauke Yahya Jammeh daga karagar mulkin da ya shafe shekara 22.

A lokacin mulkinsa, sau da yawa Jammeh kan yi biris da majalisar Gambia, inda yake kafa dokokinsa ba tare da tuntuɓarsu ba.

A ƙarƙashin sabuwar gwamnatin shugaba Adama Barrow, akwai kyakkyawan tsammanin cewa majalisar dokoki za ta riƙe muhimmin matsayin kafa dokoki.

Majalisar ministocin Adama Barrow dai ta ƙunshi shugaba bakwai na jam'iyyu daban-daban, waɗanda dukkansu sun tsayar da 'yan takara don zaɓen.

Ita ma jam'iyyar APRC da ke mara baya ga Yahya Jammeh ta shiga zaɓen, wanda al'ummar Gambia za su yi ba a ƙarƙashin Jammeh ba.

Mista Jammeh ya haifar da ce-ce-ku-cen siyasa lokacin da ya ƙi amincewa da shan kaye a zaben da aka gudanar cikin watan Disambar shekara ta 2016.

Daga bisani dai ya fice daga Gambia ranar 21 ga watan Janairun 2017, bayan ƙasashe maƙwabta sun yi barazanar tumbuke shi da kƙrfin tuwo.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Gambia Adama Barrow ya yi alwashin kawo sauye-sauye a kasar

Magajinsa Adama Barrow, ɗan kasuwa maras gogewa cikin harkokin siyasa, ya yi alƙawarin kawo sauye-sauye a fannonin siayasa da tsaron Gambia.

A wani bangare na sauye-sauyen, Mista Barrow ya kafa kwamitin tsage gaskiya da sasantawa, don bincikar cin zarafin bil'adama da aka tafka a karkashin mulkin Jammeh.

Labarai masu alaka