'Shan taba sigari ya fi ɓarna a ƙasa huɗu'

Shan taba sigari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kasar Indonesia na cikin kasashen da ke ta fafutukar hana takaita shan taba sigari

Wani sabon nazari da wasu masana suka gudanar ya ce shan taba sigari ne ke haddasa ɗaya cikin mutuwar duk mutum 10 da aka samu a duniya.

Ya ce rabin mamatan da taba sigari ke kashewa a duniya sun fito daga ƙasashen China da Indiya da Amurka da kuma Rasha.

Binciken wanda aka wallafa a mujallar the Lancet ya ce duk da shaidar da ake da ita kan illar da tabar ke da ita ga lafiya a tsawon shekara hamsin, har yanzu kimanin mutum miliyan dubu ɗaya ne ke shan sigari a kullum.

Nazarin ya ce taba sigari ce ta yi sanadin mutuwar duk ɗaya cikin duk namiji huɗu da kuma ɗaya cikin duk mace ashirin.

Duk da haka ya gano wasu ƙasashe sun yi nasara kan ƙoƙarin tallafa wa mutane wajen barin busa hayaƙin taba, akasari ta hanyar lafta mata haraji da kuma gargaɗi a maƙunsan taba, da ɓullo da shirye-shiryen ilmantar da jama'a.

Duk da irin manufofi kan takaita ko hana shan taba sigarin da suka shafe shekaru, kididdiga ta nuna cewa yawan masu shan ta ya karu matuka.

Masu nazarin sun kuma ce yawan mace-mace sakamakon cutuka masu nasaba da shan taba sigarin ka iya karuwa,muddin kamfanonin tabar suka zafafa tallata hajar ta su a kasuwanni, musamman a kasashen da suka ci gaba.