India: 'Yan sanda sun kama mutumin da ya yi saki uku

Indian Women Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan fafutuka sun ce an saki dubban mata ta hanyar saki uku rigis a lokaci guda

A kasar India 'yan sanda sun kama wani mutum a bisa zargin cin zarafi da yaudara, bayan ya saki matarsa ta biyu ta hanyar aika mata takarda ta hanyar saƙon gidan waya.

Mohammed Haneef ya aika takardar mako guda bayan aurensu. A ciki ya rubuta "talaq" (saki) sau uku.

Matarsa ta kai wa 'yan sandan Hyderabad ƙorafi, waɗanda suka ce aurensu ba ya kan ƙa'ida don kuwa ba ta bayyana cewa an sake ta da farko ba.

An ba da belin Mohammed Haneef, mai shekara 38, sai dai yanzu 'yan sanda sun ce za su tuhume shi da aikata fyaɗe.

Wani muƙaddashin kwamishinan 'yan sanda V Satyanarayana ya faɗa wa BBC cewa "Bincikenmu ya nuna cewa ƙa'idojin da aka bi aka ɗaura auren ba daidai suke ba saboda mijin ba shi da takardun da suka dace."

Mohammed Haneef yana tare da matarsa ta farko, amma rahotanni suka ce ya ƙara auren ne da yardarta.

Image caption Mata da dama a Indiya sun shiga halin tasku sakamakon sakin da ake yi musu kara-zube

Al'adar saki uku, da ke bai wa Musulmi damar rabuwa da matarsa nan take na fuskantar zazzafar adawa a India.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin mata na ci gaba da gangami don ganin an hana yin haka, yayin da kotun ƙolin India ke sauraron wata ƙara a kan yin saki uku lokaci ɗaya ya saɓa da tsarin mulki.

Masu fafutuka sun ce ƙasashen musulmi da dama ciki har da Pakistan da Banladesh sun hana saki rigis lokaci guda, amma abin yana ci gaba a India.