Me zai sa miji ya yi wa matarsa komai a duniya?

South African woman Hakkin mallakar hoto TUKU AFFAIR
Image caption Matan Afirka kamar Kgotshatso Maditse sun iya cancaɗa kwalliya da ɗaura ɗan kwali

Matan ƙasar Senegal sun yi fice wajen iya tarairaya da riƙe miji kam su shiga zuciyarsa su yi kane-kane, don haka sakin aure barkatai ya yi ƙaranci. To, ko mene ne sirrin?

Wata mai sayar da kayan kwalliya da ƙyale-ƙyale a wata kasuwar Dakar, Ami ta ce wajibi ne mata su san matsayinsu da nauyin da ke kansu a gidan aure.

Ta ce matan Senegal sun iya ado da gyaran jiki da kwarkwasa don jawo hankali a kwantar da shi ta yadda namiji zai manta da damuwa da ɓacin rai da gajiyar aikin da ya kwaso daga waje.

Tsawon shekaru dai Ami ta yi tana harkar sayar da turare da tufafin mata da sauran kayan ado da ƙyale-ƙyalen mata.

A cewarta "Matan Senegal na matuƙar darjanta kwalliya da ƙwainane da burgewa ta yadda hankulan mazansu za su tsaya a kansu."

Mijin Ami dai ya ba da shaida kan yadda matarsa ta tsere sa'a, ta zama tauraruwar da babu kamarta aƙalla a zuciyarsa.

Ya ce: ''A harkar auratayya yana da muhimmanci sosai mace ta iya faranta wa mijinta rai, ta zama maɓulɓular annuri da fara'arka a ko da yaushe."

A cewarsa in dai batu ake na iya riƙe miji, to matan Senegal ba su da na biyu,

"Ba shakka, ina farin ciki kan yadda matata ke amfani da irin waɗannan kayan gyaran jiki da na ƙyale-ƙyale suna da ƙayatarwa.''

Ina matan Senegal suka samo dabarun riƙe miji?

Matan da suka bunƙasa a harkar sayar da kayan gyara jiki da ƙyale-ƙyalen mata sun ci gaba inda suke buɗe cibiyoyi don horas da mata dabarun riƙe miji.

Cibiyoyin na mayar da hankali wajen koyar da daddaɗan girki samfurin maigida-kar-ka-taka, da ƙawata gado.

Indiya Khadi Sumare ta ce dabarun jan hankalin miji fasaha ce. Ta ce sai mace ta san yadda ake iya sanya tufafi da haɗa kaloli iri daban-daban wajen shigar da za ta sanya kafin ta iya kama mijinta.

"Dabarun janyo ɗa namiji a jiki ta hanyar taka rawa da kwarkwasa da yi wa maigida tausa duk suna taimakawa," in ji ta.

Ya abin yake a wajen matan Nijeriya

Hajiya Aisha Ibrahim Isa wadda aka sani da Aisha gyara da kanki mai sana'ar gyaran jiki ce da kwalliyar mata kuma a cewarta matan Nijeriya ma ba baya ba.

Ta ce mata sun karɓi hanyoyin gyaran jiki sosai, kuma jin daɗi da sha'awar da maza ke nuna wa matan da suke irin wannan gyaran jiki suna ƙara musu ƙaimi.

Hajiya Aisha ta ce gyaran jiki iri uku suka fi mayar da hankali kansu a Nijeriya ciki har da na ciki wanda baƙon ido ba zai gani ba sai wanda aka yi dominsa.

"Ta ce akwai wasu larurori irinsu basir da ciwon sanyi da kuma cutukan (jima'i) masu yaɗuwa, don haka muna fara magance su, ta yadda mace za ta je gidan miji lafiya lau. Miji ya taras da ita babu wata matsala."

Ƙwararriyar ta ce a baya mata sukan je wajen malaman tsibbu da bokaye ne a duk lokacin da mazansu suka fara juya musu baya, amma yanzu ta hantar gyaran jiki da iya tarairayar miji, an tsamo mata daga halaka.

A cewarta matan da suka iya gyara jikinsu ya zama mai ni'ima da ɗumi, suna samun karɓuwa sosai a wajen namiji ta yadda zai ji soyayyarta ce kaɗai ta tsaye masa zuciya. Kuma zai iya yi mita duk abin da take buƙata a rayuwa.