Suu Kyi ta musanta kisan kare-dangi kan Musulman Rohingya

Aung San Suu Kyi
Image caption Girman da ake ganin Misiss Suu Kyi da shi ya zube a idon mutane da dama kan wannan batu

Shugabar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi, ta musanta cewa ana kisan kiyashi kan Musulmi marasa rinjaye 'yan kabilar Rohingya a Myanmar, duk da yaduwar rahotonnin da ke nuna hakan.

A wata kebantacciyar hira da BBC, Suu Kyi, wacce ta lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel, ta tabbatar da matsololin da aka samu a jihar Rakhine, inda mafiya yawan 'yan kabilar Rohingya ke da zama.

Ta ce kalmar kisan kiyashi ta yi "tsauri sosai" a yi amfani da ita wajen bayyana abin da ke faruwa.

A maimakon haka shugabar ta ce kasar za ta yi maraba da duk wani dan kabilar Rohingya da ya dawo cikin kasar hannu bibbiyu.

Ta shaidawa BBC cewa, "Bana tunanin ana kisan kiyashi yanzu. Ina tunanin kalmar kisan kiyashi ta yi tsauri wajen bayyana abin da yake faruwa."

Misis Suu Kyi ta kara da cewa: "Ina tunanin akwai rashin jituwa a wurin, Musulmai ne ke kashe 'yan uwansu Musulmai, idan suna tunanin suna aiki ne da hukumomi.

"Ba wai maganar kisan kiyashi ba ne, kamar yadda ka fada, magana ce ta mutane mazauna wurare daban-daban da ke da bambanci, kuma wannan bambancin muke so mu kawar.

Ana dai hana 'yan kabilar Rohingya takardun izinin zama 'yan Myanmar, wanda aka fi sani da Burma, wanda kuma yasa ake daukar su a matsayin 'yan ci-rani daga kasar Bangladesh.

Suna fuskantar tsananin wariya daga jama'a da kuma hukumomi.

Dubban 'yan kabilar Rohingya ne dai ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira, bayan da yaki ya dai-daita su a shekarar 2012.

A watannin baya-bayan nan kusan mutum 70,000 ne suka tsallaka zuwa Bangladesh, domin tserewa hare-haren da sojojin gwamnati suka kaddamar, bayan wani harin da ya kashe wadansu 'yan sanda tara.

A watan da ya gabata ne Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa sojoji cewa suna kaddamar da hare-haren nasu ne a kan 'yan kabilar ta Rohingya, da kuma yi musu fyade, da kisan gilla, da azabtarwa. Zargin da gwamnati ta musanta.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yarinya 'yar gudun hijira kenan ke kuka a sansanin 'yan gudun hijira da ke Bangladesh

Shirun da Misis Suu Kyi ke yi a lokuta da dama kan rikicin, ya sa ta rasa darajar da take da ita, ta mai fafutikar kare hakkin dan Adam, wadda aka dade ana gode mata kan yaki da cin zarafi, lokacin mulkin sojin kasar, wanda a lokuta da dama aka yi ta kama ta.

A yanzu kasashen duniya da dama, suna kara matsa mata lamba a kan lamarin.

Amma a wata tattaunawa da ta yi a karon farko a wannan shekara, Misis Suu Kyi ta ce, ta amsa tambayoyi a kan wannan lamari a baya.

"An yi wannan tambayar tun shekarar 2013, lokacin fada na karshe ya barke a Rakhine. Kuma su ['yan jarida] za su tambayeni, kuma zan amsa musu, kuma mutane su kan ce ban ce komai ba."

"Kawai saboda ban fadi abin da mutane ke so ba, abin da mutane ke so in fada, kawai in yi Allah-wadai da wadansu mutane daban ko kuma wasu."

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ana ta yin zanga-zanga saboda hana Musulmai takardun izinin zama a kasaar

Misis Suu Kyi ta ce ba ta da masaniya game da harin watan Oktoba, amma an yi ta yada jita-jitar cewa ana kokari wajen yunkurin kawo shawarwarin zaman lafiya tsakanin 'yan Myanmar din da sauran kungiyoyin 'yan tawayen kasar.,

Kuma ta musanta cewa sojoji na yin abin da suka ga dama.

Ta ce, "Basu da damar yin fyade da kisa da azabtarwa. Suna dai da damar shiga su yi yaki, wannan kuma yana cikin kundin tsarin mulki. Harkokin soji a bar wa sojoji"

Haka kuma ta ce, sake kwace ikon a yankin ga sojoji, abu ne da gwamnati ke fatan yi. A karkashin wannan kundin tsarin mulki, sojojin na cin gashin kansu ne daga jam'iyya mai mulki.

Labarai masu alaka

Karin bayani