Har yanzu ana kashe masu sayar da shanu a Indiya

'Yan kato da gora Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Duk da sukar da firai minista, Narendra Modi ya yi a kan kungiyoyin, lamarin ya ci gaba

Jami'an 'yan sanda sun shaidawa BBC cewa wasu mutsnr sun kai harin kan wasu motoci uku da ke dakon shanu a ranar asabar.

An kai mutum biyar asibiti sakamakon jin rauni a sanadin harin kuma daya daga cikin su ya mutu a daren Talata.

Indiyawa mabiya addinin Hindu na daukar shanu a matsayin abu mai girma saboda bauta musu da wasu ke yi a kasar, kuma jihar Rajasthan da ma wasu jihohin kasar da dama sun haramta kishe shanun.

Wani babban jami'i, Parmal Gurjar ya shaida wa BBC cewa 'yan sanda sun shigar da karar kisa kan wasu wadanda ba san ko su waye ba, bayan an kashe wani mutum mai suna Pehlu Khan.

Ya ce, "Muna kallon bidiyon da aka nada domin mu gano maharan. Muna kyautata zaton 'yan kungiyar kato da gora ne da ke hana kashe shanu."

Kawun Mista Khan, Husain Khan, ya shaida wa BBC cewa Khan ba mahauci bane amma manomi ne kuma ya sayi shanun ne saboda yana sayar da madarar shanun.

'Yan sanda sun kwace motocin uku kuma sun shigar da karar mutum hudu saboda sufurin shanu kuma an haramta hakan.

Jihohi da dama na jadadda haramcin yanka shanu bayan jam'iyyar Hindu Nationalist Bharatiya Janata ta kafa gwamnatin Indiya a shekarar 2014.

A watan da ya gabata ne dai aka kafa dokar daurin rai da rai idan har aka kama mutum ya yanka sa.

Baya ga haramcin da gwamnatin kasar ta yi, kungiyoyin kato da gora wadanda suke a matsayin masu kare shanu na karfafa dokar a wasu jihohin kasar.

Kungiyoyin kan duba ababen hawa kuma su kan yi wa masu cinkin dabbobi duka.

A bara ne dai Firai minista, Narendra Modi ya soki kungiyar 'yan kato da goran, inda ya ce irin wadannan mutanen na bata masa rai.

Duk da haka wannan bai hana maharan kai harin kan masu cinikin dabbobi ba.

Labarai masu alaka