An hana MDD zuwa wurin harin da aka kai a Sudan ta Tudu

Dubban mutane sun tsere daga garin na Pajok zuwa kasar Uganda Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dubban mutane sun tsere daga garin na Pajok zuwa kasar Uganda

Masu aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan Ta Kudu sun ce a karo na biyu kenan ana hana su zuwa garin Pajok, inda ake zargin sojoji da kashe farar hula da dama.

Sun ce suna cikin damuwa game da rahoton da suka samu na yaki da kuma harin da ake kai wa farar hula. Sun yi kira da a ba su damar zuwa yankin da ke kudancin kasar.

Dubban mutane sun tsere daga garin na Pajok zuwa kasar Uganda da ke makwabtaka.

Sojoji sun musanta kai hari kan farar hular kuma sun zargi 'yan fashi da yin kisan.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar sun ce sojojin gwamnati ne suka harbe 'yan uwansu a lokacin da suke gudu, ko su kama su sa'annan su kashe su.

'Yan gudun hijira a kasar Uganda sun ce sojoji sun sauka a garin Pajok ranar Lahadi inda suka fara bude musu wuta a inda suke zaune barkatai.

Wani ya shaida wa BBC cewa sun fille wa mutane kai, da yin sata da kuma kai wa yara hari.

Kungiyar 'yan tawayen Sudan Ta Kudu, da kuma jam'iyyar National Salvation Front sun yi kira da a gudanar da bincike.

Yakin basasa na Sudan Ta Kudu ya tilastawa sama da mutum miliyan biyu barin gidajensu.

Labarai masu alaka