Kotu ta mayar wa Patience Jonathan kudinta $5.8m na banki

. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Misis Jonthan ta kai hukumar EFCC kara a baya

A Najeriya, wata kotu ta sakar wa uwargidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Patience Jonathan asusun ta na banki da ke dauke da dala miliyan 5.8.

Babbar kotun wadda take birnin Legas a Kudancin kasar, ta bayar da umurnin a sake takunkunmin da aka sanya wa asusun ajiyar Misis Jonathan da ke bankin Skye Bank, bayan da lauyoyi suka tafka muhawara kan karar da hukumar EFCC ta shigar kotun.

Hukumar ta EFCC dai ta shigar da karar neman rufe asusun Misis Jonathan ne kan abin da ta kira 'kwakkwaran zato' na cewa Misis Jonathan ta samu kudaden da ke cikin asusun ne ba bisa ka'ida ba.

Lauyan Misis Jonathan, Ifedayo Adedipe, ya ce babu ruwan uwar gidan tsohon shugaban kasar da shari'ar da ta sa aka rufe asusunta.

Mai shari'ar kotun, Mojisola Olatoregun, ta bayar da umarnin cewa a sakar wa Misis Jonathan asusunta nan da nan.

Lamarin dai ya shafi wasu kamfanoni biyar ciki har da wata Esther Oba, wadda aka ce tana da kudi har naira biliyan 7.4 a bankuna shida.

Duk da cewa wata takardar rantsuwa da wani jami'in bincike na hukumar EFCC, Abdullahi Tukur ya gabatar a kotun, ta ce akwai bukatar a yi gaggawar kwace kudaden, amma mai shari'ar ba ta gamsu da wannan bayani na masu gabatar da karar ba.

A watan Oktobar 2016 ne, uwargidan shugaba Jonathan din ta kai karar hukumar EFCC gaban kotu kan wannan batu.

Labarai masu alaka