Yadda wanzami ya illata amarya da sunan kaciya a Kano

'Yan sandan Nigeria Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan sandan sun ce za su gurfanar da mutanen a gaban kuliya

Wani wanzami ya yi wa wata amarya lahani a gabanta da sunan cire mata angurya, bayan da mai gidanta ya yi korafi ga mahifinta cewa ta ki ba shi hadin kai.

Wannan al'amari dai ya faru ne a wani kauye da ke jihar Kano a arewacin Najeriya.

An dai ce mahaifin yarinyar ne da amininsa suka nemi wanzamin domin yi mata magani ta hanyar cire mata anguryar, a inda wanzamin ya yi mata wannan aiki da karfin tsiya, al'amarin da ya janyo aka lahanta mata gabanta.

Yanzu haka dai wannan baiwar Allah ba ta iya yin fitsari ba tare da kwaroron roba ba da likitoci suka sanya ba, mata sannan kuma ana tsammanin sai an yi mata aiki kafin ta koma dai dai.

Tuni dai mutumin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, Ali Dangote ya dauki nauyin yi wa yarinyar magani, a inda shi kuma sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya tube wa dagacin garin rawaninsa.

Ku saurari rahoton Yusuf Ibrahim Yakasai domin jin abin da wanzamin da mahaifin yarinyar da ma angon nata suke fadi, bayan 'yan sanda sun kama su:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Rahoton Yusuf Ibrahim Yakasai