Amurka ta kai harin makami mai linzami Syria

Shugaban Amurka Donald Trump
Image caption Donald Trump ya nemi a taka wa Syria birki

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ya yi umarnin kai wa sansanin jiragen da suka kai harin iska mai guba kan fararen hula a Syria.

An dai ce an harba makaman masu linzami guda 51 kirar Tomahawk, inda kuma suka sauka dab da birnin Homs na Syriyar.

Shugaba Trump ya ce " Kuma bukatar Amurka ce ta dakile bazuwa da amfani da makamai masu guba ce ta sa muka aikata hakan."

Ya kuma kara da cewa " Babu wani yaron da Allah ya halitta da zai kara fuskantar irin wannan yanayi mai muni."

Mista Trump ya kara da yin kira ga kasashen duniya masu fada aji da su dauki matakin hana Syria ci gaba da yakar fafaren hula.

Sai dai kuma gwamnatin Syria na cewa kasar ta zama karkatacciyar kuka mai dadin hawa ga Amurka.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Assad na fata Amurka za ta daina katsalandan cikin al'amurran Syria

Kuma gwamnan birnin Homs ya ce abin da Amurkar ta yi musu ba shi da maraba da ayyukan ta'addanci irin na kungiyar IS da sauran kungiyoyin ta'adda.