An tsinci wata yarinya da ke rayuwa da birrai a daji

The young girl
Image caption Yarinyar a halin yanzu tana kokarin yadda za ta yi magana

'Yan sanda a Arewacin kasar Indiya na tsaka da binciken jerin sunayen yaran da suka bata, domin su gano ko akwai sunan wata yarinya da aka tsinta a daji, aka kuma yi amanna cewa da birrai take rayuwa.

Yarinyar wadda shekarunta ba su wuce takwas zuwa goma ba, an tsince ta ne a dajin Uttar Pradesh a 'yan makonni da suka gabata.

Likitoci sun ce ba ta iya magana kuma tana nuna halayyar birrai.

Wani babban jami'in dan sanda ya shaida wa BBC cewa, a lokacin da 'yan sanda suka je ceto ta, an samu yarinyar tana wasa da birrai da kuma kwaikwayon dabi'unsu.

Mutanen wani kauye ne suka gano ta a wani gandun namun daji na Katarniaghat da ke kan iyakar Indiya da Nepal, wanda ke kusa da kauyen nasu.

Jami'in dan sanda Suresh Yadav, ya ce birran sun kai wa tawagarsu hari a lokacin da suka je dauko ta.

Likitoci sun ce tana fama da rashin abinci mai gina jiki a lokacin da aka kawo ta, kuma gashinta da faratanta sun yi zako-zako, an kuma ga raunuka a jikinta.

Har ila yau ba ta iya magana sannan kuma tana yin tafiya ne a kan diga-diganta kamar yadda dabbobi ke yi.

A yanzu dai rahotanni sun ce ta fara samun sauki, kuma a karshe ana sa ran mikata ga hukumar walwalar kananan yara da sauran kwararrun ma'aikatan lafiya, domin koyar da ita dabi'un mutane sannu a hankali.

Babban jami'i mai kula da asibitin, DK Singh, ya shaida wa BBC cewa, yanzu haka yarinyar tana asibiti, amma za a mayar da ita wani babban asibitin koyarwa na Lucknow Medical College da zarar an bayar da sakamakon gwaje-gwajen da aka yi mata, domin ta samu cikakkiyar kulawa a can.

Alkalin kotun da ke yankin Ajaydeep Singh, shi ma ya ziyarci yarinyar a asibiti, inda ya ba ta suna "Forest Durga," wani suna da ake kiran wata gunkin mabiya addinin Hindu.

Yawancin 'yan Indiya na danganta yarinyar da Mowgli, tauraron wani littafin tatsuniya na "Jungle Book" wanda Rudyard Kipling ya rubuta kuma aka yi fim dinsa.

Sai dai kuma har yanzu ba a san irin rayuwa yarinyar ta yi a dajin ba.

Labarai masu alaka