Ana zanga-zangar adawa da Zuma a Afirka Ta Kudu

Afrika ta Kudu Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga daga 'yan adawa ta jam'iyyar Democratic Alliance a Johannesburg na niyyar zuwa offisin jam'iyyar ANC

Dubban masu zanga-zanga sun fito a kan tituna a manyan biranen kasar Afrika ta Kudu domin yin kira ga shugaba Jacob Zuma ya sauka daga mulki bayan da ya kori ministan kudinsa.

Mutane sun yi ta taruwa gabanin zanga-zangar a birnin Johannesburg da Cape Town da Durban da kuma babban birnin Pretoria.

Korar da Mista Zuma ya yi wa ministan kudin kasar, Pravin Gordhan ya yi sanadiyar jawowa kasar raguwar zuba jari.

Matakin da Mista Zuma ya dauka ya kara dagula yanayin matsin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Gabanin masu zanga-zangar mutane sun yi ta wallafa hotuna a shafukan sada zumunta da muhawara a ranar Juma'a Pretoria, duk da rudanin da ake samu cewa ko doka ta halatta yin zanga-zanga a babban birnin kasar.

'Yan sanda a ranar Alhamis sun ce an haramta yi zanga-zanga a Pretoria saboda mutane ba su nemi izini daga hukumomin ba. Amma daga baya wani alkali ya halatta yi hakan.

Masu zanga-zangar sun yi niyyar zuwa fadar gwamnati wato Union Buildings.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dubban mutane na zanga-zanga a birnin Durban

Amma magoya bayan Mista Zuma ma sun fito domin su kare muradun shugaban.

A wannan mako ne Mista Zuma ya yi biris da kiraye-kirayen da manyan kungiyoyin da suke kawance da jam'iyyarsa ta ANC suka yi gare shi kan cewa ya yi murabus.

A birnin Johannesburg, an zuba 'yan sanda birjik a ko ina saboda shirin da masu zanga-zangar suka yi na taruwa a gaban hedikwatar jam'iyyar ANC.

Korar minista

Matakin da Mista Zuma ya dauka na sauke Mista Gordhan daga mukaminsa ya fusata abokan adawa da kawayensa, abin da ya haddasa sabani a cikin mulkin jam'iyyar ANC, wadda ke mulki a Afrika ta kudu tun shekarar 1994.

Hakan ya sa wasu shugabanin ANC tababar ko ya kamata Mista Zuma ya ci gaba da mulkin kasar.

Magoya bayan ANC da jam'iyyar SACP da kuma babbar kungiyar kwadago ta kasar (COSATU) sun goyi bayan son Zuma ya sauka da mulki.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya sa mutane da dama hushi saboda sauye-sauye mimistocinsa

Kafofin watsa labarai a kasar sun kwatanta Mista Zuma da ''Tsuntsun mai wayo'' saboda yadda yake kaucewa yunkurin tsige shi.

Jam'iyyun adawa tare da wasu masu goyan bayan gwamnatinsa ne suka shirya wannan zanga-zangar a ranar Juma'a domin neman ya yi murabus.

Jam'iyyar Economic Freedom Fighters ta je kotu domin neman izinin tsige shi.

Labarai masu alaka

Karin bayani