Ɗan wasan Liverpool Sadio Mane zai yi jinya

Sadio Mane Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mane ya ji rauni ne lokacin da ya yi taho-mu-gama da Leighton Baines

Dan wasan gaba na Liverpool Sadio Mane ba zai buga wasanni bakwai na karshen kakar wasa ta bana ba saboda jinyar da zai yi ta raunin da ya ji a gwiwarsa.

An fitar da Mane, mai shekara 24,daga filin wasa bayan ya yi taho-mu-gama da Leighton Baines a wasan da suka doke Everton da ci 3-1 ranar Asabar.

Kocin kulob din Jurgen Klopp yana yana da "tabbacin" cewa akwai bukatar a yi wa Mane tiyata a inda ya yi rauni, kuma "hakan zai sa zai yi matukar wahala a gare shi ya sake buga wasa a kakar wasan da muke ciki".

Dan wasan, wanda liverpool ta saya a kan £34m daga Southampton ya buga dukkan wasannin da suka yi a kakar wasa ta bana idan ban da guda biyar daga cikinsu.

Sun yi kunnen doki a wasanni uku daga cikinsu, yayin da suka sha kashi a wasanni biyu. Liverpool dai ita ce ta uku a saman teburin Premier kuma tana da sauran wasannin bakwai da za ta buga.

Klopp ya ce yanzu dan wasansa Adam Lallana "yana samun sauki amma dai har bai fara atisaye ba" bayan raunin da ya yi a cinyarsa a wasan da ya yi wa Ingila a watan Maris.

Ya kara da cewa kyaftin din kungiyar Jordan Henderson, wanda ke jinya tun watan Fabrairu, yana "cikin kyakkyawan yanayi, amma ban san lokacin da zai soma atisaye ba".

Hakkin mallakar hoto @sadiomaneofficial
Image caption Sadio Mane ya wallafa hoton raunin da ya ji a gwiwarsa a Instagram ranar Alhamis

Labarai masu alaka