Russia ta soki Amurka kan harin da ta kai a Syria

Sojin ruwan Amurka sun fitar da hoton da ke nuna yadda aka kai harin Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojin ruwan Amurka sun fitar da hoton da ke nuna yadda aka kai harin

Kasar Russia ta mayar da martani cikin fushi bayan Amurka ta kai hari da makamai masu linzami a wani sansanin jiragen saman gwamnatin Syria.

Jami'an gwamnatin Amurka sun ce an yi amfani da sansanin wajen harin da gwamnatin Syria ta kai da makamai masu guba a arewa maso yammacin kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar farar hula da dama ranar Talata.

Sai dai Russia, wacce ke goyon bayan Shugaba Bashar al-Assad, ta yi tur da harin da Amurka ta kai sannan ta dakatar da wata yarjejeniya da za ta kulla da Amurka a kan Syria.

Wannan ne karo na farko da Amurka ke daukar matakin soji kai-tsaye a kan gwamnatin Syria.

An bayar da rahoton mutuwar akalla mutum shida.

Hakan ya faru ne kwana kadan bayan harin da Syria ta kai wanda ya yi sanadin mutuwar farar hula akalla 80, cikinsu har da kananan yara, a garin Khan Sheikhoun na lardin Idlib da ke hannun 'yan tawaye.

'Yan hamayyar Syria da kuma kasashen yammacin duniya sun ce gwamnatin Syria ce ta kai harin, koda yake gwamnatin ta musanta.

Labarai masu alaka