Youtube ya ƙaddamar da sabon tsarin talla

people looking at phone Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sama da mutum biliyan daya na amfani da Youtube a fadin duniya.

Manhajar Youtube ta chanja wasu dokoki ta yadda masu amfani da shafin za su fara samun kudi ta hanyar yin talla a tashoshin bidiyonsu.

Kamfanin ya ba da sanarwar cewa a sabon tsarin sai kana da masu bibiyarka da suka kai kimanin 10,000 kafin ka zama daya daga cikin masu tallata kayana jama'a a Youtube.

Haka kuma Youtube zai kimanta tashoshin ya gani ko sun yi daidai da ka'idojinsa, kafin a fara yin tallace-tallace.

Shafin Youtube ya ce hakan zai taimaka wajen rage satar abin da ya kunsa da kuma tashoshin bogi.

Babban jami'in da ke kula da harkokin gudanar da manhajar, Ariel Bardin ya rubuta a shafinsa na Youtube cewa, bayan mai shafin ya samu masu bibiya da suke bude tashoshinsu na nan take kimanin 10,000 , "za mu rika duba ayyukansu don kula da tsare-tsarenmu."

Ya kara da cewa,"Idan komai ya tafi daidai, za mu kawo tashar a tsarin "YPP", kuma za mu fara aikin tallace-tallace don kare abubuwan da ke kunshe a manhajarmu. Wadannan sabbin dokoki za su taimaka wajen tabbatar da kudaden da za su rika shiga aljihun masu shafin wadanda doka ta ba su dama.

Wata manazarciya a harkar tallace-tallace ta Kamfanin IHS, Qingzhen Chen, ta ce ba abu ba ne mai wahala a wurin wanda ya bude tashar ya samu masu bibiya da suka kai 10,000 daga cikin sama da mutum billiyan daya da suke amfani da shafin a fadin duniya ba.

A cewarta, "Ya kamata mu yi tunani a kan me ya sa shafin Youtube ya yi haka? An samu labaran matsaloli a kwanan nan game da abubuwa da ya kunsa, wasu manyan kamfanoni da hukumomi sun janye tallace-tallacensu, wannan wani kokari ne na magance ire-iren wadannan matsalolin."