An bude shafin intanet ga masu neman aiki a Nigeria

Shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Buhari ya sha alwashin magance matsalar rashin aiki

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bude shafin intanet domin miliyoyin mutanen da ke neman aiki su yi rijista.

Hukumar kididdiga kan ayyukan yi ta kasar, wacce ta bayar da wannan sanarwa, ta kara da cewa matakin zai taimaka wajen hada masu neman aiki da ma'aikatun da suka dace da su.

A cewarta, tuni shafin na www.jobsforall.ngya soma aiki.

Hukumar ta ce, "Wannan shafi zai rika tattara bayanai da duminsu kan rashin aikin yi da kuma guraben da ake da su na ayyuka. Haka kuma zai adana bayanan mutanen da ke neman aiki da kuma abin da suka kware a kansa ta yadda zai rika sada su da ma'aikatun da suka dace da su".

Sai dai hukumar ta ce tattara bayanan mutanen da ba su da aikin yi ba ya nufin zai zama hanyarsu ta samun aiki nan da nan, tana mai cewa za su jira har sai lokacin da aiki ya samu.

Najeriya ita ce kasar da ta fi yawan al'uma a Afirka, kuma hukumar kididiga ta ce akwai kimanin mutum 11m da ba su da aiki a kasar.

Labarai masu alaka