Rodgers ya sanya hannu a kwantaragin shekara hudu da Celtic

Brendan Rodgers Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Brendan Rodgers ya lashe gasar cin kofin Premier ta Scotland a Celtic

Kocin Celtic Brendan Rodgers ya sanya hannu a sabon kwantaragin shekara hudu da kungiyar.

Rodgers, mai shekara 44, ya jagoranci Celtic wurin zuwa gasar lig da kuma ta cin kofin Premier tun lokacin da ya maye gurbin Ronny Deila.

Tsohon kocin na Liverpool, Swansea City, Reading da Watford ya ce, "Na ji dadin sanya hannu a sabon kwantaragin. Wannan ce kungiyar da na fi dacewa na kasance a cikinta."

Rodgers, wanda kwantaraginsa zai kare a 2021, yana neman 'yan wasan gida domin fafatawa da Rangers a wasan kusa da karshe na gasar cin kofin Scotland a karshen watan nan.

Rodgers ya gode wa majalisar zartarwar kungiyar saboda goyon bayan da suka ba shi tun da aka nada shi.

"A matakin yin aiki da kuma na kashin kaina, zan iya cewa wannan ne wurin da ya dace na kasance. Da a shekarun baya ne zan yi saurin barin kungiyar. Amma yanzu na koyi yadda zan mutumta abin da ke hannuna."

Hakkin mallakar hoto SNS
Image caption Brendan Rodgers: "Akwai abubuwa da dama da za mu cimma"