Wasannin da za a yi a Gasar Firimiya

Jadawalin gasar Firimiya
Image caption Chelsea za ta fafata da Bournemouth

Kulob-kulob da ke wasa a Gasar Firimiya za su ci gaba da wasa a mako na 32, inda za a yi wasanni guda 10 daga ranar Asabar zuwa Litinin.

Kocin Leicester City Craig Shakespeare ya ce ya tattara hankali wuri guda don wasan da zai yi da Everton ranar Lahadi. Ya ce bai damu sosai ba, da wasan da zai yi da Atletico Madrid a Gasar Zakarun Turai ranar Laraba mai zuwa.

Ya ce: "Wasan zai yi zafi sosai. Saboda Everton ta kware yayin da take wasa a gida, har ila yau kakar bana kowa da gaske yake wasa."

Shi ma kocin Hull City Marco Silva ya fara karaya ne gabanin wasan da za su buga da Manchester City a ranar Asabar, yayin da aka ambato shi yana cewa: "Manchester City kulob ne da ya kware sosai, yana da koci mai kyau da 'yan wasa gwanaye. Muna girmama su kamar yadda muke girmama duk abokan karawarmu."

Shi kuwa kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya bayyana jin dadinsa ne game da yadda dan wasan gabansa Harry Kane wan zai dawo taka leda a karawar da za su yi da Watford ranar Asabar.

Sai dai kocin Chelsea, wadanda suke kan gaba a gasar, Antonio Conte ya ce yana jin dadin yadda masu biye musu a teburin gasar wato Tottenham za su riga su buga wasa ranar Asabar. Ya ce yana ganin hakan zai taimaka musu.

Labarai masu alaka