An soke dokar sanya takalmi coge a Canada

Gwamnatin British Columbia ta ce ba a yi wa mata adalci ba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gwamnatin British Columbia ta ce ba a yi wa mata adalci ba

Wani lardi a kasar Canada ya soke dokar da ta bukaci mata ma'aikata su rika sanya takalmi coge idan za su wurin aiki.

Gwamnatin lardin British Columbia (BC) ta ce dokar tana nuna bambanci sannan tana da hatsari ga lafiyar masu sanya takalmin.

Ta kara da cewa masu sanya takalmi coge na fuskantar hatsarin faduwa idan suna tafiya da kuma yi wa tafin kafarsu ko ma kafar tasu da bayansu lahani.

Gwamnatin ta ce ya kamata a yi takalma masu dadin sanyawa domin ma'aikata mata su rika yin aiki ba tare da fuskantar matsala ba.

An dauki wannan mataki ne bayan wani dan majalisar dokoki na jam'iyyar Green ya gabatar da kudurin dokar da zai hana wuraren aiki tilasta wa ma'aikata mata sanya takalma masu coge.

Hakkin mallakar hoto Press Association
Image caption Ana zazzafar muhawara kan sanya coge a Canada

Labarai masu alaka