'Amurka ka iya kara kai harin makami mai linzami Syria'

Donald Trump Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Trump ya ce ba za su zura ido ana kashe fararen hula ba

Jakadiyar Amurka a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya Nikki Heley, ta ce akwai yiwuwar Amurkar ta sake kai wa Syria hari, a ci gaba da martani kan yin amfani da makamai masu guba.

Misis Heley ta ce bukatar Amurka ta dakile bazuwar amfani da makamai masu guba ita ce gaba da komai, a saboda haka za su iya daukar duk matakin da ya kamata wajen hana Syria ci gaba da amfani da makaman.

Shi ma sakataren baitil malin Amurkar, Steve Mnuchin ya ce, yana duba yiwuwar kakaba wa Syriyar takunkumin tattalin arziki.

Sai dai jakadan Rasha a Majalisar ta Dinkin Duniya, Vladimir Safronkov ya bayyana harin na Amurka da wani "yunkurin yi wa dokokin kasa da kasa karan tsaye, da ka iya ta'azzara rikicin da ake yi a gabas ta tsakiya."

Ya kara da cewa, "Mun soki haramtattun matakan da Amurka ta dauka da kakkausar murya."

Tuni dai Amurkar ta ce, duk da cewa ta girgiza da martanin Rasha kan harin da Amurkar ta kai amma abin bai zo mata da mamaki ba.

Rasha dai ta bayyana harin na Amurka da wata hanyar karawa 'yan ta'adda karfi.

A ranar Juma'a ne dai shugaba Trump ya bayar da umarnin kai harin makamai masu linzami har guda 51 zuwa Syria.

Ya kuma yi hakan ne da manufar mayar da martani bisa amfani da makamai masu guba kan fararen hula da Syria ta yi.

Harin makami mai linzamin na Amurka dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane shida.

Labarai masu alaka