Russia ta ba mu kunya kan Syria — Amurka

Guided-missile destroyer USS Porter transits the Mediterranean Sea on March 9, 2017. Hakkin mallakar hoto AFP

Amurka ta ce Russia ta "ba mu kunya amma ba mu yi mamaki ba" bayan da Russia ta soke ta saboda harin Amurka ta kai a sansanin sojin Syria ranar Alhamis.

Amurka ta kai wa Syria hari ne saboda zargin da ta yi mata da kai harin sinadari mai guba a yankin da ke hannun 'yan tawaye, lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 80, cikinsu har da kanana yara.

Akalla mutum shida ne suka mutu a harin da Amurka ta kai wa Syria da makamai masu linzami ranar Juma'a da asuba.

Russia, wacce babbar kawar Syria ce, ta zargi Amurka da goyon bayan ta'addanci.

Sai dai sakataren wajen Amurka Rex Tillerson ya ce, "Na yi mamakin martanin da Russia ta mayar. Hakan ya nuna cewa suna goyon bayan gwamnatin Assad domin kai hare-hare na rashin imani kan al'umar kasar."

"Don haka ba ni kunya matuka, sai dai ban yi mamaki ba," in ji shi.

Russia dai ta yi alkawrin karfafa makaman Syria da ke kakkabo jiragen sama.