Amurka ta aike da kayan yaki zuwa North Korea

Wani jirigin ruwan Amurka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jirgin ruwa mai 'ya'ya wanda ke kunshe da jiragen yaki na sama

Amurka ta tura rundunar sojin ruwan ko-ta-kwana mai suna 'Carl Vinson Strike Group' wadda ta kunshi jiragen yaki na sama da na kasa zuwa Koriya ta Arewa.

Rundunar yakin Amurka a yankin Pacific ta bayyana tura sojin zuwa Koriya ta Arewar da matakin da ya dace na taka wa Koriyar burki dangane da barazanar da take yi wa kasashe a yankin.

Shugaba Donald Trump ya ce "Amurka ta kimtsa domin jankunnen Korea ta Arewa, ko da kuwa ba ta samu taimako ba daga kasashen duniya."

Korea ta arewa dai ta gudanar da gwaje-gwajen makamai masu linzami a 'yan kwanakin nan, al'amarin da masana ke ganin akwai yiwuwar aiwatar da karin gwajin a nan gaba.

Kuma ana tsammanin Korea ta Arewar na dab da cimma mallakar makamin nukiliya wanda ka iya tankarar da Amurka idan aka harba.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu daga cikin jiragen ruwan yaki da ke tunkarar Koriya ta Arewa

Gwajin baya bayan nan shi ne wanda Koriya ta Arewar ta yi na wani makami mai linzamin mai matsakaicin zango wanda ya sauka a tekun Japan.

An dai tsammaci China za ta dauki mataki kan gwajin da ake yi wa kallon na tsokana ne amma sai ba ta ce komai ba.

Masu lura da al'amura na danganta fargabar kwararar 'yan gudun hijra daga Korea ta Arewa zuwa Chinar da kuma tsoron ka da Amurka ta yi amfani da damar ta kutsa kai Chinar ne ya sa ta shakkar daukar wani mataki kan Koriya ta Arewar.