Harin da aka kai Cocin Masar ya kashe mutum 21

A map showing where Tanta is in Egypt

Kafafen watsa labarai na kasar Masar sun ce akalla mutum 21 ne suka mutu bayan an tayar da wani abin fashewa a wata Coci da ke arewacin kasar.

Lamarin ya faru ne a Cocin Kifɗawa ta St George's da ke birnin Tanta, arewa da Alkahira, babban birnin kasar.

Gidajen talabijin da dama na kasar sun rawaito cewa akalla mutum 40 sun samu raunuka.

Har yanzu ba a san abin da ya kai ga fashewar abin ba, amma sau da dama kungiyar IS na harar Kiristocin kasar a shekarun da suka wuce.

A watan Disamban da ya wuce, mutum 25 ne suka mutu bayan wani bam ya tashi a Cocin Kifɗawa da ke binrin Alkahira lokacin ana gudanar da ibada.

Masar ta sha fama da hare-haren masu tayar da kayar baya tun 2013 lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatin zababben shugaban kasar na farko Mohammed Morsi.

Wasu daga cikin magoya bayan Mr Morsi sun zargi Kiristoci da goyon bayan kifar da shi.

An kai harin ne lokacin da Kiristoci Kifɗawa ke bikin Palm Sunday, daya daga cikin ranaku mafiya tsarki a adddinin Kirista, domin tunawa da galabar da Almasihu ya samu ta sake shiga birnin Qudus.

Labarai masu alaka