Gidan yarin da ɗaurarru ke kasuwanci a Uruguay

A kowacce safiya, Cesar Campo yakan tashi ya yi karin kumallo cikin sauri sannan ya tafi wani wuri inda yake kera tebura da kujeru da wurin ajiye littafai, da dai duk abubuwan da masu hulda da shi ke bukata.

A kusa da inda yake yin wannan harka, makwabtansa na buga bulon kankare, wasu kuma na shuka kayan marmari, yayin da wasu ke da kantunan sayar da gahawa da biredi da kuma wurin yin aski.

Hakkin mallakar hoto Frederick Bernas
Image caption Cesar Campo zai kwashe shekaru da dama a gidan yari saboda an same shi da laifin yin fashi a banki
Hakkin mallakar hoto Frederick Bernas
Image caption Wasu daga cikin daurarrun na shuka kayan marmari domin sayarwa a waje
Hakkin mallakar hoto Frederick Bernas
Image caption An soma gidan biredi ne da kadan-kadan amma yanzu ya bunkasa
Hakkin mallakar hoto Frederick Bernas
Image caption Sau da dama ana samun layi a wannan wurin aski

Dukkan masu yin wadannan sana'o'i daurarru ne da ke zaune a gidan yarin Punta de Rieles da ke wajen Montevideo, babban birnin kasar Uruguay.

"Ba mu taba tsammanin za mu rika yin sana'o'i ba," in ji Campo, mai shekara 50, wanda ya kwashe shekara 23 a gidan yarin bayan an same shi da laifin yin fashi a wani banki.

Ya kara da cewa, "Gidan yarin na zamani ne wanda ke bai wa mutum damar da ba zai samu ba a wasu wuraren."

Akwai wani zaɓi

A daidai lokacin da ake samu yawaitar rahotannin fadace-fadace a gidajen yarin da ke Latin Amurka, musamman a Brazil inda sama da mutum 100 suka mutu a watan Janairu kadai sakamakon boren da aka yi, shi kuwa gidan yarin Punta de Rieles ya bai wa daurarrun cikinsa zabi ne kan yadda za su gyara halayensu.Shugaban gidan yarin, Luis Parodi, tsohon malamin makaranta ne wanda ya yi amannar cewa "idan yanayi ya sauya, halayen mutum ma kan sauya" kuma yana tafiyar da gidan yarin ne kan abubuwa uku: aiki, ilimi da al'ada.

Hakkin mallakar hoto Frederick Bernas
Image caption Luis Parodi (dama) tsohon malamin makaranta ne kafin ya zama shugaban gidan yari

Mr Parodi ya shaida wa BBC cewa: "Muna son bayar da rayuwa mafi inganci ta yadda daurarru za su iya yin bacci da minshari ba tare da sun ji kamar an tsane su ba ko kuma su ji tsoro."

Hakkin mallakar hoto Frederick Bernas
Image caption An kyale daurarru su rika zirga-zirga a gidan yarin har zuwa karfe bakwai na yammacin kowacce rana
Hakkin mallakar hoto Frederick Bernas
Image caption Ana barin daurarru su kai ziyara wurin abokansu da ke ciki, sanna za su iya shan shayi tare.

Da dama da cikin daurarrun 630 da ke gidan yarin Punta de Rieles sun kusa kallama wa'adin da aka dibar musu.

Hakkin mallakar hoto Frederick Bernas
Image caption Akwai cunkoso a gidajen yarin Uruguay amma Mr Parodi ba ya son daurarrun su ga kamar ana wulakanta su

Adadin daurarun da ke gidajen yarin Uruguay ya ninka tun daga shekarar 2000.

A kasar da ke da mutum 3.4 m, 10,416 daga cikinsu na zaman gidan yari bisa alkaluman 2016.

Iyali na iya kai ziyara

A gidan yarin Punta de Rieles, ana kyale daurarru su rika zirga-zirga har zuwa karfe bakwai na yammacin kowacce rana.

Da dama daga cikinsu suna da wayar salula inda suke kiran 'yan uwa da abokansu da ke waje, yayin da ake barin wasu su yi amfani da kwamputa.

Hakkin mallakar hoto Frederick Benas
Image caption Ana barin daurarru suna amfani da wayar salula a gidan yarin Punta de Rieles

A kowanne daki ana sanya mutum hudu, kuma akwai talabijin da karta da firinji da kuma kayan kida a cikinsa.

Tun daga 2015 aka soma barin 'yan uwa da abokan arziki su ziyarci daurarru sau uku a kowanne mako, har ma su zauna tare zuwa tsakar dare.

Hakkin mallakar hoto Frederick Bernas
Image caption Ana barin 'yan uwa da abokan arziki su ziyarci daurarru

Labarai masu alaka