Masu hidima a cikin jirgin Turkiya sun karbi haihuwa

Turkish Airlines stewards with baby Kadiju Hakkin mallakar hoto Turkish Airlines
Image caption Masu hidima a cikin jirgin sama na Turkiya sun taimaka wa wata mata haihuwa a yayin da ake cikin tafiya

Masu hidima a cikin jirgin sama na kasar Turkiya sun yi murna da samun karin fasinja a cikin jirginsu yayin da suke tafiya a nisan mita 12,800 daga kasa, bayan da wata mata ta haifi 'ya mace.

Wasu daga cikin fasinjojin jirgin ma sun taimaka wajen karbar haihuwar, wacce ta faru jim kadan da tashin jirgin daga Conakry babban birnin Guinea zuwa Istanbul inda za a yada zango a Burkina Faso.

An kai mahaifiyar da kuma jaririyar mai suna Kadiju, asibiti bayan da jirgin samfurin Boeing 737 ya sauka a Burkina Faso.

Rahotanni sun ce mahaifiyar da jaririyar suna cikin koshin lafiya, sai dai akwai gajiya a tare da su.

Wata sanarwa daga kamfanin jiragen saman Turkiya ta ce "Masu hidima a cikin jirgin sun ga wata fasinja mai suna Nafi Diaby, wacce ke da juna biyu na makonni 28 ta na nakuda".

Hakkin mallakar hoto Turkish Airlines
Image caption Jaririyar, Kadiju ta na cikin koshin lafiya
Hakkin mallakar hoto Turkish Airlines
Image caption An yaba wa ma'aikatan jirgin sama na Turkiya bisa yadda suka taimaka wajen haihuwar jaririyar

"Da suka ga matar ta na nakuda sai suka kai mata dauki cikin gaggawa yayin da ake tafiya a sama."

Akasarin kamfanonin jiragen sama suna kyale mata masu juna biyu su yi tafiya a jiragensu idan cikinsu bai wuce makonni 36 ba, amma ana bukatar su nuna takardar shaida daga likitansu idan cikin na su ya kai makonni 28, wacce kuma za ta nuna lokacin da ake sa rai za su haihu.