Nigeria: Fargabar bullar zazzabin Lassa a Kano

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Gwamnatin Kano ta tabbatar da mutuwar mutum biyu sakamakon cutar

Hukumomi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun musanta rahotannin da ke cewa mutum takwas sun mutu sakamakon bullar cutar zazzabin Lassa wadda bera ke yadawa, a jihar.

An dai gano wasu mutum biyu masu dauke da cutar ta Lassa a yankin karamar hukumar Tudun Wada da ke jihar.

Bincike ya tabbatar da kamuwar mutum biyun ne kawai, inda kuma sauran mutanen da ake zargi suna dauke da cutar aka sallame su.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Kabiru Ibrahim Getso ya ce kawo yanzu babu masu dauke da wannan cuta.

Sannan kuma ya ce jihar na sanya ido kan duk wadanda suka yi mu'amala da mutum biyun da cutar ta kashe domin gudun bazuwa.

Ku saurari hirarsa da Yusuf Ibrahim Yakasai:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kwamishinan lafiyar jihar Kano