Harin da aka kai Cocin Egypt ya kashe mutum 44

Taswirar da ke nuna inda Tanta yake
Image caption Egypt dai na fuskantar hare-hare daga kungiyoyin ta'adda

Akalla mutum 44 ne suka mutu bayan an tayar da wani bam a wata Coci da ke arewacin Masar.

Lamarin ya faru ne a Cocin Kifɗawa ta St George's da ke birnin Tanta, arewa da Alkahira, babban birnin kasar.

Gidajen talabijin da dama na kasar sun rawaito cewa mutane da dama sun samu raunuka.

Kungiyar IS dai ta dauki alhakin kai harin kuma da ma ta sha harar Kiristocin kasar a shekarun da suka wuce.

Kungiyar ta kuma ce ita ce ta kai harin da ya kashe mutum 25 a wata Cocin Kifɗawa da ke birnin Alkahira lokacin ana gudanar da ibada duk a ranar.

Yanzu haka gwamnatin kasar ta ayyana dokar ta-baci ta kwanaki uku a kasar.

Hakan dai zai bai wa jami'an tsaro damar neman wadanda ake zargi sannan kuma a binciki gidajensu.

Masar ta sha fama da hare-haren masu tayar da kayar baya tun 2013 lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatin zababben shugaban kasar na farko Mohammed Morsi.

Wasu daga cikin magoya bayan Mr Morsi sun zargi Kiristoci da goyon bayan kifar da shi.

An kai harin ne lokacin da Kiristoci Kifɗawa ke bikin Palm Sunday, daya daga cikin ranaku mafiya tsarki a adddinin Kirista, domin tunawa da galabar da Almasihu ya samu ta sake shiga birnin Qudus.