Ana zargin Goodluck Jonathan da karbar na goro daga Shell

Shell logo Hakkin mallakar hoto Getty Images

BBC ta ga wasu sabbin hujjojin da ke nuni da cewa manyan jami'an Kamfanin Shell suna sane suka biya gwamnatin Najeriya kudin wata makekiyar rijiyar mai, inda za a mika kudin ga wani wanda aka kama da laifin halatta kudin haram.

Haka zalika binciken ya yi nuni da cewa kudin za a kashe su ne wurin biyan 'yan siyasa cin hanci.

An kitsa lamarin ne a daidai lokacin da wani umarnin wata kotu wanda ya dakatar Shell daga ci gaba da aikin tono mai, sai dai wannan umarnin na wata kara ta daban ce da aka shigar da kamfanin kan cin hanci a Najeriya.

Kamfanin ya ce ma'aikatansa ba su yi wani abu da ya saba wa doka ba.

Rijiyar mai ta OPL 245 tana cikin gabar tekun Najeriya ne, wadda aka yi hasashen cewa tana da gangar mai biliyan tara da za a iya sayarwa a kan dala biliyan 500 a farashin gangar mai na yanzu.

Kamfanin Shell ya kai kimanin shekara 60 yana aikin mai a Najeriya, kuma yana da burin mallakar rijiyar.

Sabbin hujjoji sun nuna yadda Shell yake a shirye ya mallake su.

Dillalin da ya yi dillancin cinikayyar shi ne Dan Etete, wanda kamfaninsa ya sayi rijiyar mai ta OPL 245 a kan farashi kalilan, yayin da yake ministan man Najeriya. Daga bisani ne kuma aka kama shi da laifin halatta kudin haram a wata kara ta daban.

Sai dai Shell da kuma wani kamfanin mai na kasar Italiya, mai suna ENI, sun sayi rijiyar man OPL 245 daga hannun gwamnatin Najeriya a shekarar 2011, a kan Dala biliyan daya da miliyan 300.

Wannan kudin ya dara kasafin kudin fannin kiwon lafiyar Najeriya, sai dai ba a kashe kudin a bangaren al'amuran da suka shafi al'umma ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shell ya kai shekara 60 yana aiki a Najeriya

Daga nan ne sai gwamnati ta mika dala biliyan guda ga wani kamfani mai suna Malabu, wanda Dan Etete yake tafiyarwa.

Wasiku da aka samu daga kungiyar yaki da cin hanci Global Witness and Finance Uncovered, wanda BBC ta gani, sun nuna cewa wakilan kamfanin Shell suna daidaita da Etete shekara guda gabanin kammala cinikayya.

A watan Maris din shekarar 2010, wata wasika daga tsohon ma'aikacin hukumar leken asirin Birtaniya MI6 wanda yake aiki da Kamfanin Shell, ta nuna cewa Etete zai samu wata riba da cinikayyar.

"Etete zai samu kudi. Idan yana da shekara 70 da haihuwa, ba zai iya kawar da ransa a kan biliyan biyu da miliyan 200 to akwai matsala kuma kamata ya yi mu jinkirta har sai abin da hali ya yi."

An aike wa Babban Shugaban Zartarwar Shell, Peter Voser, kwafin wasikar da sauran manyan masu harkar mai wanda hakan ke nuni da ana da masaniya kan hannun da Etete ke da shi cikin lamarin tun daga sama.

Wakilin Peter Voser ya ki ya ce komai.

Har ila yau, Shell yana da kwararan dalilai da ke nuna cewa miliyoyin kudin za su shige aljihun 'yan siyarar Najeriya ciki har da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan.

A cikin wata wasika daga watan Yuli, ta nuna cewa wannan dai ma'aikacin Shell din ya ce shiga tsakanin da Etete ya yi "a bayyane yake cewa wani yunkuri ne na samar wa Goodluck Jonatahan kudin a kowace cinikayya da ake yi."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani mai magana da yawun Goodluck Jonathan ya ce ba shi da hannu a wannan badakala

Masu shigar da kara a Italiya sun yi zargin cewa an halatta kudin haram da suka kai dala miliyan 466 ta hanyar wasu cibiyoyin 'yan canjin kudi don biyan tsohon Shugaba Jonatahan da sauran 'yan siyasa cikin sauki.

Mai Magana da yawun Goodluck Jonathan ya shaida wa BBC cewa babu wani zargi ko wata tuhuma ko laifi ko kuma aikata ba daidai ba a gaban tsohon shugaban dangane da batun, kuma ya bayyana zargin da "kalaman karya".

BBC tana jiran martanin daga Dan Etete, sai dai a baya ya sha musanta aikata wani laifi.

Sai dai ce-ce-ku-cen da ake a kan cinikayyar ya ja hankalin jami'an tsaron a kasashen Italiya da kuma Netherlands.

A watan Fabrairun shekarar 2016, an kai samame ofishin Shell a birnin Hague inda aka kwashe wasu takardu.

A ranar da aka kai samaman, Babban Shugaban Zartarwan Kamfanin na yanzu Ben van Beurden, ya kira tsohon babban mai kula da harkokin kudin kamfanin, Simon Henry, wanda a yanzu ba ya kan kujerarsa, ta waya. Sai dai jami'an tsaron Netherlands sun nadi zantawarsu kuma BBC ta saurara.

Yayin da suke wayar, Ben van Beurden ya ce wani bincike da Shell ya gudanar ya gano wata wasika daga tsohon ma'aikatan Hukumar MI6 wanda ya bayyana da "wata maganar da aka yi a teburin shan barasa", kuma ya ce ba su taimaka ba.

Wasikun da BBC ta gani sun wuce batun da aka yi a mashaya. Suna nuna yadda wasu manyan jami'an Shell suke sane da yadda wani kamfani da Etete yake tafiyarwa zai karbi fiye da Dala biliyan guda kuma wasu ma'aikatansu sun shawarce su da cewa kudin za su tashi ne a matsayin cin hanci.

A wata sanarwa da Shell ya fitar ya ce babu wani ma'aikacinsa tsoho ko wanda yake aiki da su da ya aikata ba daidai ba.

Daga nan, ya ce idan har Malabu ta biya wasu jami'an gwamnati kudi, to an yi hakan ne ba da saninsu ba, ko da izininsu.

Kamfanin ENI bai ce uffan ba kan bukatar BBC ta ya tofa albarkacin bakinsa, amma a baya ya bayyana cewa shi ko ma'aikatansa ba su taba aikata ba daidai ba.

Za a iya tuna cewa an kitsa yarjejeniyar ne watanni kalilan bayan Shell ya biya dala miliyan 30, don sasanta wani zargin bayar da cin hanci a Najeriya da wasu wuraren.

A wani bangare na yarjejeniyar don kada a kama kamfanin da laifi a karar, Shell ya yarda zai dakatar da tono mai, ta hanyar sanya hannu a wata takarda da ya aikewa ma'aikatar shari'a ta Amurka, don daidaita al'amura da suka shafi tsaurara dokokin yaki da cin hanci a Amurka.

Abin tambaya a nan shi ne me Shell yake yi har ya fara cinikayya da wani wanda aka kama da laifin halatta kudin haram, kuma suke zargin zai kai wa tsohon shugaban kasar ne, watanni bayan sun biya kudin sulhunta wani batun cin hanci a kasar.

Matthew Page ya yi aiki da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurkan a Najeriya tsawon shekara 15. Ya shaida wa BBC: "A lokacin da ya kamata Shell ya yi dari-dari don bai dade daga cimma sulhu daga wata kara da aka gurfanar da shi ba, maimakon ya kauce wa harkokin da suke tattare da cin hanci, amma sai ya kara tsunduma."

Kotunan kasar Italiya za su yanke shawara ko su ci gaba da bin matakan fara sauraran karar da ake tuhumar Shell da kuma ENI a ranar 20 ga watan Afrilun nan.

Cin hanci da rashawa wani abin takaici ne da ya ki ci, ya ki cinye wa a Najeriya. Kuma yana da wahala a tono mai ba tare da biyan cin hanci ga 'yan siyasa ba. Kamfanonin Kasashen Yamma da masu zuba jari su ne za su yanke shawara kan ko ya dace a binciki al'amarin.

'Yan majalisa ne za su yanke shawara kan ko dokokin da suke da su a kasa, za su iya hana cin hanci.

Labarai masu alaka