Yarinyar da iyalai 50 suka yi ikirarin cewa 'yarsu ce

Jenna Cook puts up a poster to try and find her birth family Hakkin mallakar hoto Chutian Metropolis Daily
Image caption Jenna Cook ta manna hotonta don kokarin gano iyalan

Lokacin da Jenna cook ta dawo China tana 'yar shekara 20 domin neman iyayenta, ta gane ba lallai ta yi nasara ba. Abin da bata yi tsammani ba shi ne cewa za ta hadu da gomman iyalai wadanda ke fatan 'yarsu ce da ta bace.

Ranar 24 ga watan Maris na shekarar 1992, wani ya manta jaririya, wadda aka tsinta a kusa da wata tashar mota mai cunkoso da ke birnin Wuhan na kasar China.

An yi ta jira zuwa lokaci mai tsawo ko wanda ya manta ta zai dawo. Daga nan sai aka dauke ta zuwa gidan renon yara da ke birnin na Wuhan, wanda ke kusa da wajen.

A can ne aka bata suna Xia Huasi, ma'ana ''Yar China' kuma Daraktan gidan renon ya zaba mata ranar haihuwa.

Sai dai manufofin kasar a kan haihuwar yaro daya na sa iyalai na fuskantar matsananciyar wahala wajen biyan tara idan suka haifi yara da yawa. Kuma a da da kuma yanzu haramun ne a tozarta 'ya'yan shegu. Kuma ba bu wata ingantacciyar hanya a hukumance ta bayar da yara rikon yara.

Sai dai kwanaki kadan bayan haka kasar China ta yi wata doka wadda ta bai wa 'yan kasashen waje dama su karbi rikon yara, sannan kuma a karshen watan Yuni, wata malamar makarantar firamare Ba'amurkiya mai suna Margaret Cook, ta karbi rikon Xia Huasi.

Kuma ta sauya mata suna zuwa Jenna sannan daga bisani ta dauke ta suka koma Massachusetts, a Amurka.

Jenna na daya daga cikin jariran China kusan 200 da suka fara komawa cikin iyalan Amurkawa. Da yawa sun biyo baya - An yi kiyasin cewa jarirai kusan 80,000, yawancinsu mata a halin yanzu sun koma Amurka da zama, da kuma karin wasu 40,000 zuwa kasashen Netherlands da Spaniya da Ingila.

Jenna ta san cewa rikonta ake yi. Ta ce, "Muna magana kan batun rikona kamar yadda muke magana a kan abincin dare. Ban taba daukarsa a matsayin wani babban al'amari ba.

Haka kuma, wani lokaci tana mamakin daga inda ta zo.

"Da kallon cibiyarka, za ka yi tunani game da kanka: 'lallai dole a dangantani da wani jinsin mutum daban. To ko daga jikin wa na fito?

"Mafiya yawan mutane an haife su ne a iyalan da aka haife su, kuma basu taba tunani ko tababa a kan haka ba. A yayin da mutanen da ake riko ke tunanin samun sabuwar rayuwa a ko wanne lokaci."

Hakkin mallakar hoto Chutian Metropolis Daily
Image caption Jenna and her adoptive mother, Margaret Cook

Karin bayani

Jenna da 'yar uwarta, wadda ita ma aka dauko daga China, sun taso a wajen da mutane kadan ne suke kama da su. Uwar goyonsu Margaret, tana iya abin da za ta iya domin ta jaddada alaka tsakaninsu da 'ya'yanta da kuma ganin sun koyi yaren Mandarin a makaranta kuma suna yin alaka da sauran iyalai kamar nasu.

Lokacin da Jenna ke matashiya tana daya daga cikin 'yan China hudu da suk fito a wani shirin Fim a 2011, da aka sa wa suna "wani waje a tsakani." Darakta Linda Goldstein Knowlton ya dauko wata jaririya daga kasar China wadda take son ta rubuta rayuwar wadannan mata - inda aka sanya wa fim din suna "wani waje a tsakani." saboda waa kalma da Jenna ta furta cewa, "Bana tunanin cewa zan dauki kaina a matsayin cikakkiyar 'yar China ko Ba'amurkiya - kodayaushe ina so in tabbatar da daya a tsakani."

Hakkin mallakar hoto Chutian Metropolis Daily
Image caption Jenna Cook ta ziyarci gidan marayu da aka fara kai ta a shekarar 1992

Amma wani abun mamaki ya faru. Daya daga cikin matan hudu da suka fito a fil din Somewhere Between tare da Jenna, ta koma kauyen da aka tsinceta. Wata mata ta gane sakamakon hotunanta da aka wallafa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yadda ake kara-kaina a tashar bas ta Wuhan

Lokacin da ta kai shekara 20 kuma take karatu a Jami'ar Yale, an bai wa Jenna damar tafiya China domin ta fara neman iyayen nata. Hakan yana cikin bangaren binciken karatu - tana fatan binciken nata zai taimaka wa 'yan uwanta 'yan kasar China wadanda ake riko kusan 80,000 a Amurka su gano magaifansu. Amma kuma tabbas abu ne da ya shafeta, kuma ta nemi da uwar rikonta Margaret da su tafi tare.

Jenna ta wallafa hotunanta a lokuta daban-daban na shekarunta da kuma yanayi daban-daban da aka sameta. Kuma ta fara rarraba su ga jama'a a kan titunan birnin Wuhan, da yawa daga mutanen sun yi ta bayar da labaran irin hakan da suka taba ji.

Su kan yi ta ce mata"Kai, ina da wani makwabcina wanda yake da 'ya mai irin wannan yanayi,"ko "Ina da wani dan uwa wanda ya taba bayar da 'yarsa, amma ba zan iya tunawa ba ko a shekarar 1992 ne ko a 1993."

Hakkin mallakar hoto Jenna Cook

Jenna ta samu wannan daddadan labari.

Amma mutane na son labarinta, mako daya bayan zuwanta aka wallafa labarinta a jaridar kasar. An wallafa takaitaccen labarinta a shafi na biyar, sai dai kan labarin ya nuna cewa "Baba da Mama: Ina fatan rungumarku. Sannunku da kokarin kawoni cikin duniyar nan."

'Yan makonni bayan wallafa labarinta a ranar 25 ga watan Maris 2012 neman Jenna ya zama wani abu daban. Daruruwan sakonni ne suka fara zuwa ta shafukan sada zumunta.

Daga cikin sakonnin akwai wasu na gaskiya da ke nuna kamar su ne iyayen Jenna. Ta dunkule su zuwa iyalai guda 50, ko wanne daga cikinsu ya taba barin jariri a kan titi a birnin Wuhan a watan Maris na shekarar 1992.

Abun yana da matukar yawa , in ji Jenna. Amma Jenna ta yi mamaki yadda iyaye suka yi ta rububin zuwa suna cewa ita 'yarsu ce, bayan kuwa jefar da yara abu ne da ya saba ka'ida a China.

Hakkin mallakar hoto Jenna Cook
Image caption Labarin da aka wallafa a jarida a kan Jenna

Jenna dauwar rikonta sun shirya ganin iyalan nan 50 da suka yi da'awar cewa ita 'yarsu ce don ganin ko za a dace. Wasu iyayen sun zo ne su kadai, uwa da uba kawai, yayin da wasu kuwa suka zo da kafatnin danginsu.

Da yawan su kuma sun zo da hujjojin da suke ganin za su tabbatar da cewa 'yarsu ce. Amma idan suka ga alamar ba za su yi nasara ba su kan shiga mawuyacin hali na damuwa.

Hakkin mallakar hoto Chutian Metropolis Daily

A karshe dai kusan iyali 37 daga cikin 50 din nan duk sun bukaci a yi gwajin kwayoyin halitta, sai dai abin takaici dukkan su ba wanda ya nuna daidai.

Jenna ta sha matukar takaici, har ma ta yi fatan cewa da ma a ce ita 'yarsu ce.

Sai dai kuma duk da wannan kalubale, tana ganin kamar wannan bincike ya taimaka mata kwarai da gaske.

A lokacin bazarar bara Jenna ta sake komawa wani aiki China, amma ba ta mayar da hankali wajen kokarin gano iyayenta ba.

Amma ta ce, "Ina matukar son samun damar sake haduwa da iyayena na gaskiya."

Labarai masu alaka