Hotunan yadda wata mata ta je Iran daga London a Keke

Rebecca Lowe with her bike, Maud
Image caption Rebecca Lowe da kekenta kirar Maud. Rebecca Lowewith her bike, Maud

Kawayen Rebecca Lowe sun yi tsammanin ba ta cikin hayyacinta a lokacin da ta shirya yin wani bulaguro daga London zuwa kasar Iran a keke, tafiya mai nisan kilomita 11,250.

Zagayen nata ya fara ne daga nahiyar Turai zuwa Turkiyya, ta bulla ta Kudu da Masar da Sudan, daga nan ta lula kasar Oman inda bulaguron nata ya kare a Iran.

Labarin bulaguron nata da aka wallafa a shafin Turanci na BBC mai taken: Shin w, ya matukar jan hankalin dubban masu karantawa wadanda suke da sha'awar hakan.

Ta wallafa hotunan yadda bulaguron nata ya kasance.

Rebecca Lowe's bike on the Montenegro-Albania border

Ta ce, kekena kirar Maud na da cikikkiyar lafiya wajen hawa tsaunukan Prokletije da ke kan iyakar Montenegro da Albania, hawa tudun da ya kusa hallaka ni ya kuma sa na ji kamar ba zan iya kai wa ga nasara ba.

A puncture in a -3C ice-fog en route to Turkey's Taurus mountains

Na yi faci a cikin dusar kankara a kan hanyar hawa tsaunukan Taurus na kasar Turkiyya. Irin wannan lamari kuwa ya matukar yin illa ga tayoyin keken samfurin Maud bayan na yi tafiyar kilomita 5,500 a kan hanya.

An informal Syrian refugee camp in Lebanon's Bekaa Valley, near the Syrian border

Wannan wani sansanin 'yan gudun hijirar Siriya ne da hukuma ba ta san da zamansa ba, a yankin tsaunukan Beeka na kasar Labanon kusa da iyakar kasar Siriya.

Tantunan sun yi danshi kuma sun yi ruma saboda ruwan sama da kankara da ke yawan zuba, kuma ko wanne tanti daya yana dauke da kusan mutum goma.

An inadvertent detour from the main tarmac road between Amman, Jordan, and the Dead Sea

Na yi wata juyawa ta ba zata bayan na yi kokarin sauya hanya daga kan babban titin da nake kai wanda ba shi da kyan bi, wanda yake tsakanin babban birnin kasar Jordan wato Amman da tekun Dead Sea, duk da cewa hanyar a mike take sambal. Wannan wata dabara ce ta musamman da nake da ita.

Rebecca Lowe's bike in the Sahara

A zagayen da na yi a yankin Sahara a kasar Sudan na sha zafi sosai, inda rana ke takewa kwal, kuma zafin ya kai ma'aunin selshiyas 40.

A wannan lokacin ruwan guzurina ya kare, kuma ruwan jikina ya fara kafewa, amma daga baya na dawo hayyacina sakamakon taimakona da wasu iyalai 'yan kabilar Nubiya da ke yankin Kudancin Masar suka yi.

Vendors and a rogue interloper at the camel market near Khartoum

Sun bata min hoto! Wadannan wasu masu sayar da kayayyaki ne da masu wucewa suka shiga cikin hoton na so dauka a kasuwar rakuma kusa da Khartoum babban birnin Sudan.

Ana sayar da kusan rakumma 350 a matsayin nama sau biyu a duk mako, an shaida min cewa, ko wanne daya a kiyasce yana kai wa fam 850.

Sudanese tea ladies in Khartoum

Wasu matan kasar Sudan suna shan shayi a birnin Khartoum, wadanda suke yawan fuskantar wariyar launin fata da kuma cin zarafi daga 'yan sanda. A shekarar 2016, Awadiya Mahmoud (daga dama) ta samu nasarar lashe kyautar mata masu kwazo ta duniya ta kasar Amurka, sakamakon kirkiro da kungiyar taimakon mata masu sana'ar shayi.

Shia Muslim Bandari women from southern Iran wearing embroidered Boregeh masks.

Mata 'yan shi'a daga kudancin Iran sanye da nikabi wato abin rufe fuska.

A puncture in the Iranian mountains

Na sake yin faci a tsaunukan kasar Iran, kusa da Abyaneh, inda tayar kekena ta baya ta kara lalacewa. Sai dai na yi sa'ar samun taimako daga wasu masu kiwon tumaki, wadanda suke shafe sa'o'i suna aikin auna amfanin gonarsu.

Dukkan hotunan mallakin Rebecca Lowe ne.

Kuna iya bin Rebecca a shafinta na Twitter @reo_lowe

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba