Larabawa sun bai wa Trump sabon suna 'Abu Ivanka'

Screengrab of Facebook post by Basel Karzoun

Asalin hoton, Facebook/Basel Karzoun

Bayanan hoto,

An yi zanen hoton Trump sanye da hular Larabawa

Larabawa a shafukan sada zumunta sun yi ta godewa shugaban Amurka Donald Trump tare da san ya masa sabon suna, Abu Ivanka, saboda harin da Amurkan ta kai kan Siriya.

Sai dai su kuma Amurkawa sun yi ta bayyana fargabar kada hakan ya sa su fada cikin yaki tare da ganin zakewar shugaban, inda har suka kirkiro da maudu'in #AmericaIsOverParty a shafukan sada zumunta.

Abu Ivanka al-Amreeki

Larabawan dai sun yi ta farin ciki da annashuwa bayan da Mista Trump ya kaddamar da harin farko kan dakarun gwamnatin Siriya.

Amurkar ta kaddamar da harin ne a kan sansanin dakarun saman Siriya, a safiyar ranar Juma'ar da ta gabata, bayan da aka zargi gwamnatin kasar da kai harin makami mai guba kan yankin da ke karkashin ikon 'yan tawaye.

Jim kadan bayan hakan ne, wasu Larabawa masu amfani da shafukan sada zumunta suka fara kiran Mista Trump din da Abu Ivanka - wato ma'ana Baban Ivanka, a matsayin Alkunya da martabawa.

Wasu kuwa ma sun yi ta kiransa da Abu Ivanka al-Amreeki - ma'ana Baban Ivanka, Ba'amurke, kamar yadda ake yi wa Musulmai lakabi.

Sai dai wasu na sukar lamirin harin shugaban tare da abin da hakan zai haifar.

Wani mai amfani da shafin sada zumunta, ya zana hoton shugaban ta hanyar sanya masa rawani (irin na wasu Malaman Musulunci), da kalmar "Muna sonka"

Kuma an bayyana shi da cewa, "Mai cika alkawari", yayin da wani mai amfani da shafin ya ce, "A 'yan watanni kadan ka yi abinda Obama ya kasa yi a shekara takwas."

Asalin hoton, Facebook/@HazmKSA1

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wani mai amfani da shafin Twitter ya ce, "Jiragen yaki 15 wadanda suka hallaka dubban 'yan Siriya" aka lalata a harin, ya sauya hotonsa na facebook da fuskar Trump, da kuma tutar Amurka, da kuma kalmomin Larabci na "Muna sonka."

Wani mai gwagwarmaya a kafafen yada labarai a Idlib, na fatan ganin karin hare-hare, inda ya yi kira ga shugaban na Amurka da ya ci gaba da kai hare-hare "har sai an sauke Assad"

Yayin da wasu ke cewa "ba sa tsammanin" wannan rana za ta zo, sun gode wa Trump saboda yin "abin da matsoratan shugabanin Larabawa suka kasa yi."

Wani dan Siriya ya wallafa a shafinsa cewa, "Muna fata da sannu za ka shiga zukatanmu. Mun gode maka Trump."

Wani dan Siriya mazaunin London ya ce, "A karon farko cikin shekara shidgwamnati Assad ta fara girbar abin da ta shuka."

Wani dan Siriya mai zane-zane mazaunin Houston, Moustafa Jacoub ya wallafa hoton kauna ga shugaban na Amurka.

Asalin hoton, Facebook/Moustafa Jacoub

Wani dan Jaridar Siriya Rami Jarrah ya ce, "'Yan Siriya ba su taba yaba wa wani dan Adam ba kamar Trump, kawai suna murna ne cewa Assad zai rasa karfin da zai rika kashe su."

Wani mawallafi a shafin intanet kuma mazaunin London Karl Sharro, wanda rabinsa dan Lebanon ne rabi kuma dan Iraki, ya ce, "Trump ya yi saurin fahimtar siyasar Amurka: Idan abubuwa suka rincabe a gida, sai a fara shirin soji a gabas ta tsakiya "

Wani mutum ya kara da cewa, "To yanzu kuna son Trump? Ina mutanen da suka rika cewa idan ya ci zabe zai tsani Larabawa da Musulmai?"

Wani mai goyon bayan gwamnatin Siriya, kuma mai sukar harin na Amurka, ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, "Shin Trump zai iya kai hari sansaninsa, baya ga duk yaran Iraki da Siriya da suka hallaka a Raqqa da Mosul?"

#AmericaIsOverParty - Amurka na zakewa

Asalin hoton, Twitter/@IslaAltamirano

Wasu mazauna Arewacin Amurka na tunanin Amurka na neman wuce makadi da rawa. Yayin da suke fargabar fadawa cikin mummunan yaki, sun yi ta raba hotuna da bidiyo, tare da yin suka a shafin twitter da maudu'in #AmericaIsOverParty.

An yi ta amfani da mabambantan maudu'ai a baya, kamar su #TrumpIsOverParty da #HillaryIsOverParty,

Asalin hoton, Twitter/@k3vxn_

Mutane a Amurka sun yi ta wallafa raha a shafukan sada zumuntar inda suke nuna cewa idan abin da Trump ya yi ya jawo yaki, to za su tattara ya-nasu-ya-nasu zuwa kasashen da ke makwabtaka da Amurkar don neman mafaka.

Sai dai bayan dariya da raha, da yawa sun ce suna, "Jin tsoron aukuwar yakin a zahiri".

Ana amfani da maudu'an ne domin yin hanunka-mai-sanda ga shugaban da magoya bayansa.

Wani mai amfani da shafin ya ce, "Ya kamata mutanen da suka zabi Trump su fara shiga aikin soji," yayin da wani ya ci gaba da cewa "Bana cikin lissafin Trump, saboda haka ba za a turani wannnan yaki ba."

Bangaren da ke kula da mu'amala da shafukan sada zumunta na BBC World Service ne ya rubuta wannan labari.