Trump zai sayar wa Nigeria jiragen yaki

A watan Fabrairu ne Msita Trump ya kira shugaba Buhari ta waya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A watan Fabrairu ne Mista Trump ya kira shugaba Buhari ta waya

Shugaban Amurka Donald Trump zai aiwatar da shirin sayar wa da Najeriya jiragen yaki domin ta yaki Boko Haram duk da fargabar da ake nunawa kan batun kare hakkin bil'adama.

Jami'an gwamnatin Amurka sun ce an dauki matakin ne domin karfafa wa dakarun Najeriya gwiwa a yakin da take yi da masu tayar da kayar bayan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum sama da 30,000.

Idan cinikin ya tabbata, Najeriya za ta sayi jiragen yaki samfurin Embraer A-29 Super Tucano kan kudi dala miliyan 600.

Ana sa ran Shugaba Trump zai mika bukatar yin hakan a hukumance nan da 'yan makonni ga majalisar dokokin Amurka domin neman amincewa.

Najeriya da Amurka sun kitsa yarjejeniyar ne lokacin mulkin tsohon Shugaba Barack Obama, sai dai ba ta fara aiki ba lokacin.

A watan Janairun bana, wani jirgin saman soji ya yi kuskuren kai hari a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke arewa-maso-gabashin kasar, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jirgin yakin samfurin Embraer A-29 Super Tucano ne wanda kudinsa ya kai dala miliyan 600

Shugaba Trump da takwaransa Muhammadu Buhari sun tattauna batun sayar da makaman ne a wata ganawa ta waya da suka yi a watan Fabrairu.

Gwamnatin Najeriya ta sha cewa yakin da take yi da Boko Haram yana fuskantar cikas daga tanade-tanaden dokokin Amurka.

Amurka ta tura wa Najeriya wasu sojoji wadanda za su taimake ta da shawarwari kan yaki da masu tada kayar bayan.

Sai dai bisa tanadin wata dokar Amurka wadda aka yi wa lakabi da Leahy Law, Amurka ba za ta iya sayar wa Najeriya makamai ba saboda zargin take hakkin dan Adam da ake zargin dakarun kasar da aikatawa, kodayake hanin ya shafi duka kayan aiki ne.

Har ila yau, dokar ta yi hani ga sauran kasashe da kada su sayar wa Najeriya makamai saboda yarjejeniyar da suka kulla da Amurkan.