Pakistan ta yanke hukuncin kisa ga dan leken asirin Indiya

A ranar 29 ga watan Maris na shekarar 2016, manema labarai a Islamabad na kallon bidiyon kama Kulbhushan Jadhav, wanda ake zargin dan leken asirin Indiya ne.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jami'in kasar Pakistan ya ce mutumin cikin bidiyon dan leken asirin kasar Indiya ne

Wata kotun soji a kasar Pakistan ta yanke wa tsohon jami'in sojin ruwa na kasar Indiya hukuncin kisa, bayan samunsa da laifin leken asiri.

Tun a bara ne hukumomin na Pakistan ke tsare da Kulbhushan Jadhav.

An kama Kulbhushan ne a lardin Balochistan wanda ke fama da rikici, kuma aka zarge shi da "leken asiri da zagon-kasa a kasar Pakistan".

Ba a dade da kama shi ba ne kuma kasar ta saki wani bidiyo wanda ke nuna cewa yana da hannu a leken asirinta.

Indiya ta ce mutumin dan kasarta ne, sai dai ta musanta zargin cewa dan leken asiri ne.

Pakistan na zargin Indiya da goya baya ga 'yan awaren Balochistan da ke tayar da kayar baya kuma wurin ne Pakistan ta tsare Mista Jadhav a ranar uku ga watan Maris na shekarar 2016.

Wata sanarwar da ma'aikatar yada labarai ta rundunar sojin kasar ta fitar ta yi karin haske da cewa "Kotun sojin Pakistan din ta yanke wa dan leken asirin hukuncin kisa ne bayan samunsa da laifi a karkashin dokar soji ta kasar. Sai dai ba a bayyana lokacin da za a aiwatar da hukuncin kisan ba.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"Zaman kotu na shirme"

India has condemned the sentence and called the proceedings against Mr Jadhav "farcical".

Kasar Indiya ta yi watsi da hukuncin kisan, inda ta bayyana shi da cewa "Shirme ne."

Ma'aikatar wajen Indiya ta ce "An sace Shri Jadhav ne kasar Iran a bara kuma babu wani bayani kan yadda ya samu kansa a Pakistan."

Haka kuma an hana Jami'ai ganinsa duk da bukatar hakan da suka yi a hukumance sau 13, kuma ba a sanar da Indiya cewa ana yi masa shari'a ba.

Sanarwar ta kara da cewa, muddin aka aiwatar da hukuncin to za ta dauke shi a matsayin "Kisan kai"

Makwabtan masu makaman nukiliya na da tsohon tarihin dangantakar diflomashiyya mai tsami, sannan dukkansu sun sha zargin tura wa juna 'yan leken asiri.

A watan Nuwamba Pakistan ta janye jami'anta shida daga ofishin jakadancinta da ke birnin Delhi, bayan da Indiya ta kore su a bisa zargin cewa 'yan leken asirin ne.

It later leaked to the press the names and photos of eight alleged Indian spies working from India's mission in Islamabad.

Daga bisani kuma ta bai wa manema labarai sunaye da kuma hotunan mutum takwas da take zargin 'yan leken asirin Indiya ne da ke aiki a ofishin jakadancin kasar da ke Islamabad.