Sojoji sun yi ba-ta-kashi da mahara a Nijar

Niger army Hakkin mallakar hoto Getty Images

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa wasu mutane sun kai wa dakarun sojin kasar da ke zaune a wani sansani mai nisan kilomita biyu daga gGarin Geskerou yankin Diffa Hari.

Sai dai Sojin Na Nijar sun yi nasarar kashe Maharan da dama suka kuma jikkata wasu.

Ana kyautata zaton cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai harin.

Sai dai ba asarar rayuka a bangaren dakarun sojin Nijar din amma sun rahotanni sun ce sama da sojoji 10 ne su ma suka yi rauni.

Kawo yanzu dai ba wani abun da da ya yito daga hukumomin yankin kan wannan hari, sai dai shaidun gani da ido sun ce sun ga gawawwakin 'yan kungiyar ta Boko haram birjik ga kasa.

An dai kwashe sama da sa'a 2 ana ta barin wuta tsakanin bangarorin biyu.

Yankin Diffa mai makwabtaka da tarrayar Najeriya na fuskantar matsalar hare-hare daga 'yan kungiyar Boko Haram.

Daga watan Fabrairun shekarar 2015 sun kadamar da hare-hare da dama aNijar, abun da ya yi sanadiyar mutuwar dakarun sojin kasar da fararen hula da yawa, wasu kuma suka kauracewa matsugunansu.

Gwamantin kasar Nijar tare da hadin gwiwar sauran kasashen yankin tafkin Chadi sun kafa wasu rundunoni don yaki da wannan kungiya.

Labarai masu alaka