Tony Adams ya zama sabon kocin Granada

Tony Adams Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Adams ne sabon kocin kulob Granada

An nada tsohon dan kwallon Ingila kuma tsohon kyaftin Arsenal, Tony Adams kocin Granada har zuwa karshen kakar bana.

Mista Adams ya maye gurbin Lucas Alcaraz, wanda aka kora a ranar Litinin bayan sun sha kashi 3-1 a wasan da kungiyar ta yi da Valencia inda ya mayar da su matsayin na 19 a La Liga.

Mista Adams mai shekara 50 ya yi aiki da kulob din Sipaniyan tun watan Nuwamba, kuma shi ne mataimakin shugaban kamfanin Granada din.

Wasansa ta farko zai kasance a gida ne inda za su kara da kungiyar Celta Vigo a ranar Lahadi.

Adams ya babr kulob din Gabala na Azerbaijan a shekarar 2011, inda daga baya ya jagoranci kungiyoyin Wycombe Wanderers da Portsmouth.

Adams ya yi wasanni 669 a Arsenal tsakanin shekarar 1983 da 2002, inda ya shafe shekara 14 yana aiki a matsayin kyaftin din kungiyar, ya kuma ci wa Ingila wasanni 66.

Labarai masu alaka

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba