Faransa: Mummunar gobara a sansanin 'yan gudun hijira

Bayanan bidiyo,

Kusan bukkoki 300 da ke sansanin sun lalace

Wani sansanin 'yan gudun hijira da ke dauke da mutum 1,500 a Arewacin Faransa ya lalace sakamakon wutar da ta tashi, wadda jami'ai suka ce ta tashi ne a lokacin da ake wani fada tsakanin 'yan Afghanistan da Kurdawa.

A kalla mutum 10 ne suka jikkata lokacin da wutar ta fara kama bukkokin da ke cikin sansanin na Grande-Synthe, kusa da tashar jiragen ruwa ta Dunkirk.

A watan da ya gabata ne jami'ai suka ce za a rushe sansanin saboda yawan tashe-tashen hankula da ake yi a wajen.

Arewacin Faransan da ke kusa da teku ya zama wani dandali ne na 'yan gudun hijirar da ke kokarin shiga Birtaniya.

Wani jami'i mai kula da wannan yanki Michel Lalande, ya ce, "Ba bu abin da ya yi saura a sansanin sai tarin toka."

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, AFP/Getty

Asalin hoton, AFP/Getty

Ya kara da cewa, "Zai yi wahala a iya sake gina bukkokin kamar yadda suke a da."

Yawan al'ummar da suke sansanin Grande-Synthe ya karu tun watan Oktabar bara da aka lalata sansanin 'yan gudun hijira na Jungle da ke kusa da Calais, kimanin kilomita 40 daga nan.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito jami'ai da ganau suna cewa, zuwan 'yan Afghanistan da dama ya sa an samu karuwar tashe-tashen hankula tsakanin su da Kurdawa da suke zama a sanasanin.

Mista Lalande ya kuma ce tuni aka kwashe 'yan gudun hijirar kuma za a kai su masaukan gaggawa, inda aka tanadar musu wuraren motsa jiki har biyu a kusa da wajen.

An sha samun rikice-rikice a sansanin Grande-Synthe, wanda kungiyar Likitoci ta Doctors Without Borders ta gina shi, aka kuma bude shi a watan Maris din 2016.

Kusan mutum shida ne aka ji musu rauni da wuka, bayan da aka fara fadan wanda ya jawo gobarar.

Kamfanin AFP ya ce, 'Yan sanda sun shiga tsakani a watan da ya gabata, bayan da aka ji wa wasu mutum biyar rauni a wani fada, aka kuma dabawa wani mutum wuka a watan Nuwamba.