An samu rubabben jemage a cikin Salak a Amurka

Hoton mataccen jemage

Asalin hoton, FANK209

Bayanan hoto,

Sai bayan da mutum biyun suka fara cin salak din sannan suka gano rubabben jemagen

Shagon Walmart da ke Amurka ya yi kira ga masu sayen kayayyaki a shagon su dawo da salak da suka saya bayan wasu da suka saya a jihar Florida sun gano wani rubabben jemage a cikin kwalin Salak din.

Jami'ai sun ce kwastomomin biyu sun ci kadan daga cikin salak din kafin su gano jemagen, kuma an yi musu gwaji domin a tabbatar da cewa ba su kamu da cutar rabies da ake kamuwa da ita ta hanyar alaka da wasu dabobbi ba.

Kamfanin ya aika da umarnin cewa, duk wadanda suka sayi salak, wanda akasari ake sayarwa a jihohin kudancin Amurkan, su zubar da shi.

Walmart ya kuma ce za a iya mayar wa mutane kudinsu idan har sun bukaci hakan.

Cibiyar kare yaduwar cututuka ta kasar CDC, ta ce sai da mutanen biyu suka fara cin salak din kafin su gano rubabben jemagen.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An gano cewa mutanen biyu da suka ci salak din ba su kamu da cutar Rabies ba bayan da aka yi musu gwaji

Cibiyar CDC ta yi wa jemagen gwajin cutar rabies.

A wata sanarwa da cibiyar CDC din ta fitar, ta ce duka mutunen biyu suna cikin koshin lafiya kuma sakamakon gwajin ya nuna cewa babu wani a cikinsu da ke dauke da alamomin cutar rabies din.

Cibiyar ta kuma bayar da shawarar cewa duk wanda ya ci salak din kuma ya tsinci wani bangare na dabbar a ciki ya "gaggauta zuwa asibiti".

Kamfinin Walmart ya yi aiki tare da ma'aikatansa domin fitar da duka salak din da ke shagon a lokacin, kuma baya ga salak din babu wani abu da ke da matsala a shagon.