An kori kocin Argentina Edgardo Bauza bayan wasa takwas

Edgardo Bauza

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A watan Agustan da ya gabata ne Argentina ta nada Edgardo Bauza

Argentina ta sallami kocinta Edgardo Bauza bayan ya jagoranci tawagar kasar sun buga wasa takwas, ba tare da samun tabbaci ba kan ko za su samu damar zuwa Gasar Cin Kofin Duniya da za yi badi a kasar Rasha.

Kasar ita ce ta biyar a jerin kasashen yankin kudancin Amurka da suke neman samun damar zuwa gasar, wanda guda hudu ne kawai suke da tabbacin zuwa gasar. Hakan yana nufin idan ta kare a matsayi na biyar, sai ta yi nasara a wasan da za a hada ta da wata kasa daga nahiyar Oceania, kafin ta samun damar shiga gasar.

An zabi Bauza mai shekara 59 a watan Agustan bara kuma a karkashin jagorancinsa ne tawagar ta yi rashin nasara sau uku, sanna kuma ta yi kunnen doki biyu, suka kuma samu nasara sau uku.

"Mun shaida wa Bauza cewa an dakatar da shi a matsayin kocin tawagar", inji Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Argentina Claudio Tapia.

"Tawagar ba ta wasa yadda ya kamata kuma kowa ya san hakan".

Wasan karshe da Bauza ya jagoranta shi ne wanda Bolovia ta doke Argentina da ci 2-0, wanda hakan ya zo bayan an hana Lionel Messi buga wasanni hudu bayan ya zagi wani jami'in wasa.

A yanzu, Argentina na da ragowar wasannin hudu da za su yi kafin su cancanci shiga gasar, inda za su buga wasansu na gaba da Uruguay a ranar 31 ga watan Agusta.

Raban da Argentina ta kasa zuwa Gasar Cin Kofin Duniya tun shekarar 1970.