Nigeria: An gurfanar da shugaban kungiyar Ansaru a kotu

Al-Barnawi
Bayanan hoto,

Al-Barnawi a kotun gabannin mai shari'ar ya karasa

An gurfanar da shugaban kungiyar Ansaru, wadda ta balle daga kungiyar Boko Haram, Khalid Al-Barnawi, a gaban wata babbar kotu a Abuja, babban birnin Najeriya, inda ake tuhumar sa da ta'addanci da kisan gilla da sace mutane.

Tuhumar da ake masa ta shafi sace wasu mutane 'yan kasashen waje 10 da ake zargin kungiyar tasa da yi.

Amman Al-Barnawi ya musanta tuhume-tuhumen da ake masa da wasu mutum shida.

Mai shari'a John Tsoho na babbar kotun tarayyar Najeriyar da ke Abuja ya bayar da damar kare masu shaida kamar yadda masu gabatar da kara suka nema.

Lauyoyin gwamnati sun kuma nemi alkalin ya ba wa gwamnati damar tsare wadanda ake tuhumar a wani wuri na musamman sabili da tsaro.

An daga zaman kotun zuwa ranar 25 ga watan Afrilu domin yanke hukunci kan damar tsare mutanen a wani gidan wakafin da ba gidan yarin da ke karamar hukumar Kuje na birinin tarayyar Najeriya, Abuja ba.

Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya sun tafi da wadanda ake tuhumar bayan an daga zaman kotun.

Su waye Ansaru?

Kungiyar Ansaru ta zama barazana a kasar cikin dan kankanin lokacin da ta shafe tana ayyukanta, inda ta yi amfani da dabaru da karfi wajen shiga muhallan da ke cike da tsaro don sace mutane da yin garkuwa da su, wadanda daga baya ta ce ta kashe bakwai daga cikinsu.

A watan Janairun 2012 ne aka kirkiro kungiyar Ansaru, duk da cewa ba a san ta ba sai bayan wata shida da kafuwarta, sakamakon sakin wani bidiyo da ta yi da ya nuna yadda 'yan kungiyar suka sha alwashin kai wa Turawa 'yan kasashen yamma hari, domin kare Musulmai a duniya.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a watan Janairun 2012, ta ce, "A karon farko muna farin cikin sanar da al'umma kafuwar wannan kungiya wacce taka kafa ta kan hujjoji na kwarai."

Sanarwar ta kara da cewa, "Za mu yi aiki ba sani ba sabo a kan komai, domin mu goyi bayan da abin da ayke da kyau mu kuma yada shi, sannan kuma mu kyamaci abin da ba shi da kyau, mu kuma kawar da shi."

Cikakken sunan kungiyar shi ne, Jama'atu Ansarul Muslimina Fi Biladis Sudan, wato: "Kungiyar Kare Musulmai bakake a nahiyar Afirka".