Nigeria: Shell ya tabbatar da hannunsa a 'cinikin boge'

Shell

Asalin hoton, Getty Images

A karon karfo Kamfanin Shell ya amsa cewa ya yi hulda da wani wanda ake zargi da hallarta kudin haram yayin cinikin wata makekiyar rijiyar mai a Najeriya.

Kamfanin Shell ya amsa hakan ne bayan wasu wasikun email sun nuna cewa kamfanin ya yi hulda da Mista Dan Etete, wanda daga bisani aka same shi da laifin halatta kudin haram a wata kara ta daban.

Shell da wani kamfanin Italiya sun biya dala biliyan daya da miliyan 300 ga gwamnatin Najeriya don su mallaki rjiyar man.

Masu bincike suna zargin an biya fiye da Dala biliyan daya ga wani kamfani da Mista Etete yake tafiyarwa.

Kamfanin Shell da kamfanin Italiya ENI sun kulla wata yarjejeniya da gwamnatin Najeriya don mallakar rijiyar mai, mai lamba OPL 245, wato wata makekiyar rijiyar mai da ke gabar ruwan yankin Neja-Delta da ke Najeriya.

Daga nan ne sai gwamnatin Najeriya ta mika kudin ga wani kamfani mai suna Malabu, wanda Mista Etete yake tafiyarwa, kamar yadda masu gabatar da kara a Italiya suka bayyana.

Wasu bayanai da masu gabatar da kara a Italiyar suka gabatar sun yi zargin cewa an halatta kudin haram da suka kai dala miliyan 466 ta hanyar biyo da su ta kasuwar 'yancin kuxi, inda daga nan aka mika wa tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da wasu mukarrabansa.

A lokutan baya idan aka tambayi Shell game da batun, yana cewa ne ya biya kudin ne ga gwamnatin Najeriya don warware wata shari'a da ta ki ci, ta ki cinyewa game da batun mallakar rijiyar mai ta OPL.

Sai dai a yanzu mai magana da yawun Shell ya ce kamfanin taba hulda da Kamfanin Malabu da kuma Mista Etete gabanin kulla yarjejeniyar.

"A tsawon shekaru, Kamfanin Shell ya yi kokarin ya fahimci tsare-tsaren Malabu, ciki har da matsayin Mista Etete a kamfanin," inji shi.

Ya ci gaba da cewa: "A tsawon lokaci ta bayyana karara a garemu cewa Etete yana da hannu a Malabu kuma hanya guda da za a warware kullin shi ne ta hanyar shigo da Etete da Malabu, ko muna so, ko ba ma so. Kuma hakan shi ne matsayin gwmnatin Najeriya."

"Daga dimbin bangarori da suka shiga yarjejeniyar, mun fahimci gwamanntin Najeriya za ta saka wa Malabu da wani abu don mallakar rijiyar man. Kuma mun yi amannar cewa sulhun da gwamnati wani abu da shari'a ta san da shi," inji shi.

'Magana ta sauya'

Bayanan hoto,

Shell ta kai shekara 60 tana aiki a Najeriya

An samu sauyi ne bayan da Kungiyar yaki da cin hanci ta Global Witness and Finance Uncovered da wasu kungiyoyin rajin yaki da cin hanci, suka wallafa wasu wasikun email wadanda BBC ta gansu, suna cewa ne wakilan Shell sun fara tattaunawa da Mista Etete ne shekara guda gabanin cimma yarjejeniyar.

An turawa Babban Shugaban Kamfanin Peter Voser kwafin wasikun wadanda suke nuna cewa manyan kamfanin suna sane aka shigo da Etete cikin yarjejeniyar.

Ma'aikacin Global Witness, Rachel Owens, ya ce: "Shell yana yawan cewa ya biya kudi ga gwamnatin Najeriya ne kawai. Amma a yanzu sai Shell ya sauya maganarsa."

A lokacin da Shell ya cimma yarjejeniyar mallakar rijiyar mai ta OPL 245, ma'aikatar shari'ar Amurka ta dakatar da shi daga ci gaba da aiki, saboda warware wata kara kan cin hanci.

Sai dai wakilan Peter Voser ba su ce uffan ba tukuna. Kuma Kamfanin ENI ya ce babu wasu hujjojin da ke nuna cewa wani daga cikin ma'aikatansa ya aikata ba daidai ba.

Mai Magana da yawun Goodluck Jonathan ya shaida wa BBC cewa babu wani zargi ko wata tuhuma ko laifi ko kuma aikata ba daidai ba a gaban tsohon shugaban dangane da batun, kuma ya bayyana zargin da "kalaman karya".

BBC tana jiran martanin daga Dan Etete, sai dai a baya ya sha musanta aikata wani laifi.