Goodluck Jonathan ya ƙaryata karbar cin hanci daga Shell

Shell

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya karyata zargin da ake masa cewa ya karbi dala miliyan 200 a matsayin cin hanci daga manyan kamfanonin mai na Shell da ENI, sakamakon cinikin wata rijiyar mai a gabar teku da ke yankin Naija Delta a kasar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun tsohon shugaban, Ikechukwu Eze, ya fitar, ya ce wadannan zarge-zarge duk 'labaran bogi ne', wadanda aka kirkiro da nufin bata sunan Mista Jonathan a idon kasashen duniya.

Mista Jonathan ya ce bai san tsohon ministan mai na kasar Dan Etete ba, wanda shi ne ya kitsa wannan yarjejeniya mai cike da rudani, ya kuma karbi makudan kudi daga kamfanin Shell a cinikin wannan rijiyar mai, wadda aka ce mallakinsa ce.

Sai dai a cewar ma'aikatan Shell a wani rahoto, sun yi ikirarin cewa Mista Jonathan da Mista Etete sun san juna tsawon shekaru, tun lokacin da Mista Jonathan ya koyar da 'ya'yan Mista Etete lokacin yana ministan mai.

Kamfanin Shell dai ya musanta cewa ya aikata ba daidai ba.

A cewar masu shigar da kara na Italiya, gwamnatin Najeriya ta mika kudin da Shelll da ENI suka biya dala biliyan 1.1 ga wani kamfani Malabu, wanda yake karkashin ikon Mista Etete.

Wasu bayanai da masu gabatar da kara a Italiyar suka gabatar sun yi zargin cewa an halatta kudin haram da suka kai dala miliyan 466 daga cikin kudin ta hanyar biyo da su ta kasuwar musayar kudi ta bayan fage, inda daga nan aka mika wa tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da wasu mukarrabansa.

Mai magana da yawun Mista Jonathan ya ce an fara yarjejeniyar sayen rijiyar man ne tun gabannin ya hau mulki.

"Ya kamata mutane su yi aiki da hankali don su fahimci cewa, cinikin da aka yi da Malabu an fara shi ne tun kafin Jonathan ya hau mulki, don haka ba zai yiwu a ce ya karbi na goro ba a abin da aka yi baya nan ba," in ji shi.

'Magana ta sauya'

Bayanan hoto,

Shell ta kai shekara 60 tana aiki a Najeriya

An samu sauyi ne bayan da Kungiyar yaki da cin hanci ta Global Witness and Finance da wasu kungiyoyin rajin yaki da cin hanci, suka wallafa wasu wasikun email wadanda BBC ta gansu, suna cewa ne wakilan Shell sun fara tattaunawa da Mista Etete ne shekara guda gabanin cimma yarjejeniyar.

An turawa Babban Shugaban Kamfanin Peter Voser kwafin wasikun wadanda suke nuna cewa manyan kamfanin suna sane aka shigo da Etete cikin yarjejeniyar.

Ma'aikacin Global Witness, Rachel Owens, ya ce: "Shell yana yawan cewa ya biya kudi ga gwamnatin Najeriya ne kawai. Amma a yanzu sai Shell ya sauya maganarsa."

A lokacin da Shell ya cimma yarjejeniyar mallakar rijiyar mai ta OPL 245, ma'aikatar shari'ar Amurka ta dakatar da shi daga ci gaba da aiki, saboda warware wata kara kan cin hanci.

Sai dai wakilan Peter Voser ba su ce uffan ba tukuna. Kuma Kamfanin ENI ya ce babu wasu hujjojin da ke nuna cewa wani daga cikin ma'aikatansa ya aikata ba daidai ba.

Mai Magana da yawun Goodluck Jonathan ya shaida wa BBC cewa babu wani zargi ko wata tuhuma ko laifi ko kuma aikata ba daidai ba a gaban tsohon shugaban dangane da batun, kuma ya bayyana zargin da "kalaman karya".

BBC tana jiran martanin daga Dan Etete, sai dai a baya ya sha musanta aikata wani laifi.