'Tozarta yara wajen kai harin ƙunar-baƙin-wake ya ƙaru'

UNICEF

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rahoton ya ce ƙananan yara har ma da jarirai na shiga tarko ƙungiyar Boko Haram inda ake amfani da su wajen kai hari

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi gargadi game da ƙaruwar amfani da yara wajen kai hare-haren ƙunar-baƙin-wake da Boko Haram ke yi.

A cikin wani sabon rahoto na wata ukun farkon shekara ta 2017, UNICEF ya ce an kai harin ƙunar-baƙin-wake 77 a Nijeriya, da Chadi, da kuma jamhuriyar Kamaru.

Ƙasashen da suka fi fama da hare-haren ƙungiyar Boko Haram a yankin tafkin Chadi.

Bayanan hoto,

Hare-haren ƙunar-baƙin-wake sun yi sanadin mutuwar mutane da lalata dukiya masu yawa

Rahoton ya kuma ce adadin ƙananan yaran da aka yi amfani da su wajen kai harin ƙunar-baƙin-wake a rikicin ya kai 27 a wata ukun farkon bana.

Kawo yanzu dai in ji rahoton, an yi amfani da yaro 117 wajen kai harin ƙunar-baƙin-wake a wuraren taruwar jama'a a fadin kasashen Nijeriya da Chadi da Nijar da kuma Kamaru tun daga 2014.

Ya ce an samu 4 a shekara ta 2014, 56 a cikin 2015, da kuma 30 a shekara ta 2016, sai kuma 27 a watanni ukun farkon wannan shekara.

Hakan dai ya jefa rayuwar ƙananan yara har ma da jarirai cikin halin gaba kura baya siyaki. Don kuwa sun zama abin tsoro a kasuwanni da wuraren binciken ababen hawa, inda ake tunanin suna dauke da ababen fashewa.

Bayanan hoto,

Hare-haren ƙunar-baƙin-wake sun yi sanadin mutuwar mutane da lalata dukiya masu yawa

Babbar jami'ar Asusun mai kula da yankunan yammaci da tsakiyar Afirka Marie-Pierre, ta ce wannan shi ne tozarta ƙananan yara mafi muni da aka taba samu a rikice-rikice.

"Wadannan yaran ba su da laifi, sanya su ake yi, ana yaudararsu, ko tilasta musu aikata wanann mummunan abu.''

A wasu hirarraki daban-daban da ya gudanar, UNICEF ya ce kananan yara da dama da kan yi mu'amala da ƙungiyar Boko Haram, kuma sukan boye mawuyacin halin da suka shiga a hannun Boko Haram, saboda fargabar nuna musu kyama.

UNICEF din ya kuma yi nuni da kalubalen da mahukunta ke fuskanta da kananan yaran da aka cafke a wuraren binciken ababen hawa, kuma ake rike da su a wasu cibiyoyin gwamnati daban-daban tsawon lokaci.

A shekara ta 2016, ana rike da yara kusan 1,500 a cibiyoyin gwamnati a kasashen Nijeriya, da Chadi, da Kamaru da kuma Nijar.