Amurka ta nemi gafara bisa kalamanta kan Hitler

Sean Spicer

Asalin hoton, Getty Images

Sakataren Yada Labaran Fadar White House Sean Spicer ya nemi gafara bayan ya yi ikirarin cewa Adolf Hitler bai yi amfani da makami mai guba ba, a lokacin Yakin Duniya na Biyu.

Mista Spicer ya ce: "Ina tunanin idan ana maganar amfani da makami mai guba, Hitler bai yi amfani da shi ba a kan jama'arsa kamar yadda Assad ya yi a kan tasa jama'ar".

Sai dai sabanin ikirarin Mista Spicer, an ruwaito cewa an yi amfani da makami mai guba wajen kashe Yahudawa da sauran mutane lokacin kisan kiyashin Holocaust da aka yi lokacin Yakin Duniya na Biyu.

Bayan mutane sun yi Allah-wadai da kalamansa a shafin sada zumunta na Twitter, tare da yin nuni ga yadda Hitler ya yi amfani da makami mai guba kan Yahudawa da mazauna Jamus da kuma abokan adawarsa na jam'iyyar Nazi, Spicer ya nemi afuwa.

"Na yi kuskuren kawo misalin da bai dace ba kan kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa domin babu wata alaka tsakaninsu. Saboda haka ne nake neman gafara. Kuskure ne fadin hakan."

Mista Spicer ya sha sukar kasar Rasha game da goyon bayan da take bai wa gwamnatin Siriya.

Bayanan hoto,

An yi ta sukar sa a shafin Twitter

Fadar White House ta ce Rasha tana kokarin kaucewa daukar laifi kan harin makami mai guba da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 89.

Hukumar leken asirin Amurka ta ruwaito cewa gwamnatin Siriya ta kai hari da makami mai guba.

Sai dai Siriya ta musanta zargin, ita kuma Rasha ta ce'yan tawaye ne suka jawo harin saboda su ne suka boye makamai masu guba, wadanda suka tarwatse bayan da aka kai hari a kansu.

Daga nan ne sai Amurka ta kai wasu hare-hare a wani sansanin dakarun Siriya.