Iran: Ahmadinejad zai tsaya takara duk da gargadin Ayatollah

Mahmoud Ahmadinejad ya yi rijista a zaben shugaban kasar Iran (12 April 2017)

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Mahmoud Ahmadinejad ya ce gargadin kawai "shawara ce"

Tsohon shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinejad, ya cike takardar tsayawa takara, a zaben shugaban kasar da za a yi a watan Mayu, duk kuwa da gargadin da jagoran addinin kasar ya yi masa na kada ya yi hakan.

Mista Ahmadinejad, wanda ya mulki kasar karo biyu a tsakanin shekarar 2005 da 2013, ya cike takardar tsayawa takara a zaben na 19 ga watan Mayu ne a ma'aikatar cikin gidan kasar.

A shekarar da ta gabata jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei ya gargade shi da ka da ya yi hakan, "don ba abun da ya dace da shi da kuma kasar ba ne".

Amma dai Mr Ahmadinejad, ya fada wa maneman labarai ranar Talata cewa, "Wannan kawai shawara ce."

'Yan Jaridar kamfanin dillanci labarai na Associated Press wadanda suka shaida lokacin da Mista Ahmadinejad ke rijistar tsayawa zaben, ranar Talata sun ce jami'an zaben sun yi "mamaki" lokacin da ya gabatar da takardar tasa.

Sai dai har yanzu shugaba Hassan Rouhani, mai matsakaicin ra'ayi wanda ya cimma yarjejeniyar nukiliya da manyan kasashen duniya a shekarar 2015, bai yanki takardar tsayawa takarar ba, amma kuma ana tsammanin zai nemi tsaya din a karo na biyu.

Wata kafar yada labaran kasar ta ce sama da 'yan takara 120 ne ciki har da mata shida suka mika sunayensu a ranar farko da aka fara tantance 'yan takarar.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Hukumar zaben za ta sanar da sunayen 'yan takarar da suka yi nasara ramar 27 ga watan Afrilu

Idan aka gama sayar da takardun tsayawa takarar ranar Asabar, hukumar za ta tantace 'yan takarkarun ta bangaren siyasa da addinin.

Hukumar zaben za ta sanar da sunayen 'yan takarar da suka yi nasara ranar 27 ga watan Afrilu.

Da yake magana bayan mika takardar tsayawar tasa, Mista Ahmadinejad ya ce, ya mayar da hankali wajen cika alkawarin da ya yi na kin tsayawa takara, kawai dai yana son goyon bayan tsohon mataimakinsa ne Hamid Baqai, wanda ya yi rijista tare da shi.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mista Ahmadinejad Ya ce "na tsaya kakara ne kawai saboda in goyi bayan Baqai

Ya ce, "Na tsaya takara ne kawai saboda in goyi bayan Baqai, kuma zan yi aiki da shawarar jagoran addini. Zan yi amfani da karfina wajen yi wa Mista Baqai aiki."

Ya kara da cewa, "Wasu mutane na cewa shawarar jagoran addinin, na nufin haramta min tsayawa gaba-daya, amma abin da yake cewa kawai shawara ce".

Ayatollah Khamenei, ya ce ya fada masa kar ya tsaya ne, saboda tsayawar tasa za ta "haifar da zazzafar adawa, wadda za ta jawo rabuwar kan kasar, wanda kuma na yi amanna cewa ba abu ne mai kyau ba".

Kin kara zabar Mista Ahmadinejad a shekarar 2009, ya haifar da babbar zanga-zanga a Iran wacce ba a samu kamar ta ba tun lokacin juyin-juya halin kasar a shekarar 1979.

Miliyoyin mutane ne suka bukaci a sake zaben, amma jagoran addinin ya tabbatar da sakamakon zaben, kuma ya bayar da umarnin murkushe 'yan adawa wanda hakan ya janyo mutuwar dubban 'yan adawa da raunata da dama daga cikinsu.