An kai wata kububuwa 'yar ƙwaya gidan kaso

kububuwa

Asalin hoton, CORRECTIVE SERVICES NSW

Bayanan hoto,

Ba za a iya ambatar sunan kububuwar ba saboda dalilai na shari'a

A lokacin da 'yan sandan kasar Australiya suka kai samame wani dakin gwaje gwajen kimiyya, sun yi tsammanin za su kwato kilo-kilo na kwayar da ka iya sa bacci ta Narcotics ta makudan kudi.

Sai samamen da suka gudanar ya gano wani abu daban: Sun gano katuwar kububuwa da ta nuna alamun 'yar kwaya ce. Sun gano cewa kububuwar ta shaki kurar kwayar a jikinta.

Watanni bakwai bayan haka, kububuwar mai cike da fushi ta yi sanyi bayan da masu zaman gidan yari 14, wadanda aka zaba domin bai wa dabobbi kulawa su bata kulawa.

Kububuwar na daga cikin dabobbi 250 da ake kula da su a wani gida kaso da ke Sydney babban birnin Australiya, wanda ke da wasu dabbobin da dama.

Cibiyar kula da dabbobi ta John Morony Correctional Complex tana kula da dabbobi masu jan jiki da aka kwato a lokacin da 'yan sanda suka kai samame.

Asalin hoton, CORRECTIVE SERVICES NSW

Bayanan hoto,

Ian rike da wani maciji da aka kula da shi a gidan kason

A cewar daya daga cikin jami'an cibiyar kula da dabbobin, wasu masu aikata miyagun laifuka kan yi amfani da macizai masu dafi domin su tsare musu bindigogi da kwayar da suke boyewa.

Da zarar an kammala shari'ar da ake yi da wadanda ake zargi da safarar kwaya, za a kai kububuwar, wacce ba za a iya ambatar sunanta ga wasu mutanen daban ba.

Gwamnan gidan yarin, Ivan Calder ya ce shirin kula da dabbobin, wanda aka shafe shekara 20 ana yi, yana taimakawa wajen sauye tunanin 'yan gidan yarin.

Ivan ya shaidawa BBC cewa, "Mun lura cewa, mu'amalar da ke tsakanin 'yan gidan kason da dabbobin na sakawa su zamo masu saukin kai".

Asalin hoton, CORRECTIVE SERVICES NSW

Bayanan hoto,

Daya daga cikin 'yan gidan kason da ya kula da dabbobi

Ya kuma kara da cewa, hakan na bai wa masu zaman gidan yarin damar bayar da kulawa da kuma daukar nauyin dabbobin na taimaka musu wajen sauya halayarsu".