'Yan Taiwan sun shiga 'mummunan' hali saboda hana su cin mage da kare

Wani kare a keji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Taiwan ta gabatar da sabbin dokoki domin inganta dokar dake kare lafiyar dabbobi a kasar

Majalisar dokokin kasar Taiwan ta amince da wani kudirin doka da ya hana yanka kyanwowi da karnuka da nufin ci.

Kudirin dokar ya kuma hana mutane daure dabbobin da suka saba da su jikin motocinsu a matsayin jagororinsu a lokacin da suke tafe.

Za a ci tarar duk wanda ya saba wannan dokar makudan kudi ko kuma a daure shi tsawon shekara biyu a gidan kaso kuma a wallafa sunayensu da hotunansu ta yadda mutane za su gane su.

An dauki wadannan matakai ne domin inganta dokar dake kare dabbobi a kasar.

Matakin da aka dauka a ranar Talata wani muhimmin cigaba ne a dokar dake kare dabbobi a kasar kuma wannan ne karo na farko da aka yi doka irin wannan a Asiya.

A shekarar 2001 ne Taiwan ta zatar da dokar da ta hana sayar da nama da fatar dabbobi kamarsu kyanwowi da karnuka saboda abinda ya kwatanta da " dalilin tatalin arziki.

A baya dai ana yawan cin naman kare a tsibirin, amma a yanzu ana ganinsa a matsayin wata dabba abokin zaman mutane.

A shekarar da ta gabata ne shugabar Taiwan, shugaba Tsai Ing-wen ta karbi rikon wasu karnuka da a baya ake amfani da su a matsayin 'yan jagora tare da kyanwowinta guda biyu, Cookie da A-Tsai.

Ms Tsai, wacce ita ce mace ta farko da ta shugabancin kasar, ta ja hankulan mutane a lokacin da abinda suka kira " iyali na farko".