An kama ''yan IS' da ke shirin kai hari ofisoshin jakadanci a Nigeria

Mayakan Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

DSS ta ce 'yan IS din na da alaka da mayakan Boko Haram

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS ta ce ta kama wasu 'yan kungiyar Boko Haram da ke alaka da 'yan IS da ke yunkurin kai hari a ofisoshin jakadancin Amurka da Burtaniya a kasar.

Sanarwar da mai magana da yawun DSS, Tony Opuiyo ya fitar, ta ce jami'anta sun kai samame a wurin da 'yan kungiyar ta Boko Haram, suke a jihar Benue da kuma Abuja, babban birnin kasar.

Ta ce an kai samamen da aka kama mutanan ne a tsakanin ranakun 25 da 26 ga watan Maris kan wani gungun 'yan Boko Haram da ke da alaka da ISIS a jihar Benue da Abuja.

Hukumar ta ce mutanen sun kammala shirin kai hari a ofisoshin jakadancin Burtaniya da Amurka da wasu kasashen yammacin duniya da ke Abuja.

DSS ta kara da cewa lokacin da ta kai samamen ta kama 'yan kungiyar biyar: Isa Jibril da Jibril Jibril da Abu Omale Jibril da Halidu Sule da kuma Amhodu Salifu.

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ce ya yaba wa DSS da sauran jami'an tsaron kasar a kan yakin da suke yi da ta'addanci da tabbatar da tsaro.

Sannan ya ce Amurka da Najeriya za su ci gaba da kulla kyakkyawar alaka ta yaki da 'yan ta'adda.

Shi ma ofishin jakadancin Birtaniya ya fitar da sanarwa inda ya ce, "Muna matukar godiya ga gwamnatin Najeriya kan goyon bayan da take ba mu na yadda hukumomin tsaron kasar ke ba mu kariya a kasar."

Kazalika, DSS ta ce jami'anta sun kama wani dan kungiyar Boko Haram a garin Fika na jihar Yobe ranar 22 ga watan Maris, wanda ya amince cewa suna shirin kulla wata aika-aika.

Hukumar ta ce ma'aikatanta sun cafke wasu 'yan kungiyar Ansaru a farkon watan Afrilu a jihar Edo.

Sannan ta ce ta tabbatar cewa suna da alaka da Abu Uwais, wani babban dakaren kungiyar Ansaru wanda ya yi kaurin suna wajen addabar jihohin Kogi da Edo.

DSS ta ce jami'an nata sun kama wasu mutanen da ake zargi da aikata laifuka a jihohi daban-daban, tana mai yin kira ga 'yan Najeriya su rika sanya idanu sosai domin gano marasa gaskiya.

Birnin Abuja ya fusknaci hare-harhe a baya ciki har da wanda aka kai ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin a 2011, wanda ya kashe mutum sama da 20.