Kalli bidiyon yadda EFCC ta kwato N13bn a Lagos

Kalli bidiyon yadda EFCC ta kwato N13bn a Lagos

A ranar Laraba ce hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa EFCC, ta gano wasu makudan kudi lakadan da bata taba samun irinsu ba lokaci guda a wani tafkeken gida da ke unguwar Ikoyi, a birnin Lagos da ke Kudancin kasar.

Kudin wanda yawansu ya kai dala miliyan 4.3 da fam miliyan 27,800 da kuma naira miliyan 23.3, an gano su ne yayin da hukumar ta kai samame a gidan da ba kowa a cikinsa.

Jumlar kudin gaba daya ya kama naira biliyan 13.

Samamen ya biyo bayan wani bayanan sirri da ofishin hukumar reshen jihar Lagos ya samu ne daga masu fallasa bayanan sirri, inda suka shaida wa EFCC cewa suna zargin irin shige da ficen da ake yi da manyan jakankuna a gidan.