Kotu ta miƙa wa gwamnati kuɗin da EFCC ta kama

Bayanan bidiyo,

Ku kalli bidiyon yadda EFCC ta gano kudin da ba ta taba gano irinsu ba

Wata babbar kotun tarayyar da ke Lagos na Najeriya ta mika wa gwamnatin kasar makudan kudin da hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC ta kama a birnin ranar Laraba.

EFCC ta gano zunzurutun kudin ne $43,449,947, £27,800 da kuma N23,218,000 a wani tafkeken gida da ke unguwar Ikoyi, a birnin na Lagos.

Jumlar kudin gaba daya ta kama naira biliyan 13.

Kotun, karkashin jagorancin mai sharia Muslim Hassan, ta amince a bai wa gwamnatin kasar kudin a matsayin wucin gadi.

Alkalin ya dage sauraron kara kan batun zuwa ranar biyar ga watan Mayu mai zuwa, ko da za a samu mutumin da zai yi ikirarin mallakar kudin.

EFCC dai ta ce ta gano kudin ne yayin da ta kai samame a gidan, wanda babu kowa a cikinsa.

Samamen ya biyo bayan wani bayanan sirri da ofishin hukumar reshen jihar Lagos ya samu ne daga masu fallasa barayi, inda suka shaida wa EFCC cewa suna zargin irin shige da ficen da ake yi da manyan jakankuna a gidan.