An kori manyan jami'an NNPC kan sakaci

NNPC ya yi kaurin suna wajen cin hanci

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

NNPC ya yi kaurin suna wajen cin hanci

Babban kamfanin mai na Najeriya, NNPC ya kori wasu manyan jami'ansa hudu bisa samunsu da laifin sakaci da aiki.

A wata sanarwa da NNPC ta fitar ranar Alhamis ya ce ya yi wa jami'an Mrs. Esther Nnamdi-Ogbue, Mr. Alpha P. Mamza, da kuma Mr. Oluwa Kayode Erinoso ritaya.

Sai dai wata majiya ta shaida wa BBC cewa an kori jami'an ne saboda samunsu da sakaci wurin aiki lamarin da ya yi sanadiyar 'batan' man fetur wanda ya tasamma kusa da naira biliyan goma sha daya ba.

Majiyar ta ce jami'an hudu sun shigo da man fetur da ya kai lita miliyan 100, inda suka ajiye shi wasu gidajen mai, kamar yadda aka saba, a yunkurin gwamnati na samar da isasshen mai.

Amma daga bisani man ya yi batan dabo, lamarin da ya sanya NNPC ya kafa kwamitin da a karshe ya gano cewa mutanen sun yi sakaci har masu gidajen man suka sayar da shi ba tare da saninsu ba, kana ba su mayar wa NNPC shi ba.

NNPC dai ya yi kaurin suna wajen zarge-zargen cin hanci, inda a yanzu haka ake tuhumar tsohuwar ministar man kasar Diezani Alison-Madueke da laifin sace makudan kudade.